Noura Hussein: An soke hukuncin kisan da aka yanke mata

Noura Hussein Hakkin mallakar hoto Amnesty International
Image caption Noura Hussein za ta yi zaman gidan kaso na shekara biyar

Wata kotun daukaka kara a Sudan ta soke hukuncin kisa da aka yanke wa matar da ta kashe mijinta da ta ce yayi mata fyade.

Noura Hussein mai shekara 19 za ta yi zaman gidan kaso na shekara 5 ne a maimakon a kashe ta, inji lauyanta Abdelaha Mohamad.

Mahaifiyarta Zainab Ahmed ta fada ma BBC cewa ta yi murna da aka soke hukuncin kisan akan 'yar tata.

Shahararrun mutane daga kasashe da dama sun rika yin wani kamfe na neman a saki matar, inda suka rika amfani da kalmar #JusticeforNoura a shafukan intanet.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akan yi ma wasu 'yan matan Sudan aure tun suna da kananan shekaru

A watan jiya ne wata kotun Islama ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar ratayewa bayan da ta same ta da laifin mijinta mai suna Abdulrahman Mohamed Hammad babu dalili.

Uwargida Noura Hussein ta fada ma kotun cewa mijin nata ya kira wasu 'yan uwansa wadanda suka rike ta a yayin da shi kuma yayi mata fyade.

Amma da ya dawo kashegari yana bukatar maimaita fyaden, sai ta nemo wuka domin kare kanta kuma a sanadiyyar haka ne ta yanke shi, wanda ya zama ajalinsa.

An dai yi ma matar auren dole ne tun tana 'yar shekara 16, kuma mijin nata dan uwanta ne wanda ya girme ta da shekara 16.