Me ya sa 'yan China ke ba da akwatin gawarsu?

Akwatin gawa Hakkin mallakar hoto Beijing News
Image caption An lalata dubban akwatunan gawa a kudancin lardin Jiangxi

Wani kamfe da ya nemi mazauna yankunan karkara a China su ba da akwatin gawarsu domin kona gawa saboda inganta muhalli na janyo ce-ce-ku-ce a kasar.

Shafin yada labarai na The Paper a karshen makon jiya ya bayyana cewa mazauna lardin Jiangxi fiye da dubu hamsin sun mika akwatunan gawarsu a karshen mako, inda wasu rahotanni suka ce an "tilasta wa" wasu yin haka ne.

Kafofin watsa labarai sun rika yada hotunan akwatunan gawa da aka yi da katako da aka tara a cikin wata mota mai kafafuwa uku ko kuma ana sauke su kasa daga benaye a garin Gao'an.

China na kokarin ganin ta sauya tunanin mutane kan al'adar binne gawa kuma tana son ta karfafa musu gwiwa wajan kona gawa domin magance matsalar rashin wadataccen fili.

A bisa al'ada, al'ummar kasar sun yi itifakin cewa binne gawa ita ce "hanyar da ta ce a bi kan mamaci" in ji kamfanin dilancin labarai na Xinhau.

Al'ummar kasar na zuba jari sosai a bangaren binne gawa da kuma akwatin gawa kuma sun yi ammanar cewa yin wannan wata hanya ce ta mutunta magabata.

'Yunkurin sauya yadda ake binne gawa

Hakkin mallakar hoto Neil Beckerman
Image caption Gwamnati ta fi so a rika kona gawa maimakon binne ta

A cewar shafin The Paper, wata mota mai kafa uku ta rika bin gida-gida a garin Gao'an a karshen mako tana karbar akwatin gawa daga gidajen mutane.

Shafin ya ce wani mazaunin yankin mai shekara 94, wanda yake da matsalar ji, ya ce bai san abinda ke faruwa ba, sai bayan da aka gabatar masa da wata takarda kuma aka fada masa cewa an sauya tsarin binne gawa na yankin.

"Ba tare da ba ta lokaci ba ya mika akwatin gawarsa, wanda ya adana da dadewa," in ji shafin The Paper.

Jaridar Global Times ta ce an biya mazauna yankin diyyar Yuan 2,000 (kimanin dala 308) kan kowane akwatin gawa da aka mika.

Sai dai ta ce kudin bai taka kara ya karya ba, idan aka dubi yawan kudin da mazauna yankin suka kashe wajan yin akwatin gawa, inda ta ce akasarin mutane kan kashe Yuan 3,000 domin gina akwatin gawar.

A wasu yankunan karkara ana samun mutane masu yawa wadanda suka sa a yi musu akwatin gawa tun da wuri, a cewar jaridar Global Times .

Jaridar ta kara da cewa wadanda ba su ba da akwatin gawarsu ba za a ci su tara.

Wannan shi ne abin da ya faru a watan Afrilun da ya gabata, inda aka lalata akwatin gawa na katako fiye da 1,000 a garin Shangrao, kamar yadda jaridar Global Times.

'Abin takaici'

Masu amfani da shafin Sina Weibo sun rika sukar matakin sauya tsarin binne gawa da aka dauka a lardin Jiangxi.

A makon da ya gabata dubban mutane ne suka bayyana ra'ayoyinsu a shafin, inda suka rika sukar rashin tausayin matakin inda wasu suka ce raba mutane da akwatin gawarsu "abin takaici ne."

"A idon gwamnati, al'umma ba mutane ba ne," in ji wani mai bibiyar shafin.

Wani kuma da ke amfani da shafin ya kira labarin "mai sosa rai " wani kuma ya ce, "Na dade ina karanta labarai amma babu wanda ya tayar mini da hankali kamar wannan."

'Yawan masu kona gawa zai kai kashi 100 kafin shekarar2020'

Hakkin mallakar hoto Beijing News
Image caption Ana karfafa gwiwar iyalai a kan su rika amfani da kabari guda daya

An tattara bayanai game da matsalar da China take fuskanta wajen neman wurin da za ta binne gawar mamata.

A watan Afrilun shekarar 2016, shafin kamfanin dilancin labarai na Xinhau News Agency ya bayyana cewa ana fuskantar matsalar a Beijing babban birnin kasar.

"Galibin makabartan da ake da su sun cika, a kan haka mutane na zuwa garurua makwabta domin bine 'yan uwansu. Kashi 80 na filayen makabarta a garin Hebei da ya kewayen Beinjing an sayar da su ga mazauna Beijing," in ji kamfanin dillancin labaran.

Sai dai kasar ta bullo da wani tsari da zai magance matsalar nan da shekara biyar.

A shekarar 2016 ma'aikatu tara na gwamnatin China suka fitar da sanarwar hadin gwiwa, inda suka zayyana matakan da gwamnati za ta bi wajen binne gawa domin rage amfani da fili kafin shekarar 2020.

Gwamnatin ta kara zage dantse wajen ganin an rika jefa gawa a cikin teku ko kan bishiya - inda za'a tabbatar cewa an shuka bishiya a wurin da aka kona gawar mamaci.

A birane masu fama da yawan al'umma gwamnati ta ba da shawarar yin kaburbura kusa da juna kuma ba masu fadi sosai ba.

Kuma ta karfafa gwiwar iyalai a kan su rika amfani da kabari guda daya.

Sai dai burinta shi ne mutane su daina binne gawa, sun rungumi kona gawa.

Ma'aikatar kula da abubuwan da suka shafi jama'a ta shaida wa wata kafar watsa labarai a shekarar 2014 cewa "tana son ta ga yawan masu kona gawa a kasar ya kai kashi 100 cikin 100 kafin shekarar 2020".

Labarai masu alaka