Ba a yi min adalci kan rikicin Fulani - Buhari

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Kalli aka kona dukiya a rikicin jihar Filato

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi korafin cewa ba a yi masa adalci game da yadda ake cewa ba ya daukar mataki kan Fulanin da ake zargi da kashe mutane saboda shi ma Bafulatani ne.

Shugaban, wanda ya yi korafin a lokacin da ya kai ziyara jihar Filato inda aka kashe mutane sama da 200 a harin da aka kai wasu kauyukan jihar, ya ce bai dace ba a "daura masa laifin abin da makiyaya masu bindiga ke yi domin ana ganin ya yi kama da su".

Ya ce : "Ya kamata a lura cewa 'yan Najeriya da yawa sun yarda cewar duk da kalubalen tsaron da ake fuskanta, wannan gwamnatin ta samu muhimman nasarori a bangaren tsaro."

Shugaban ya ce shi zai ci gaba da matsa wa jami'an tsaro wajen ganin cewa sun tabbatar da tsaro a duk fadin kasar.

Shugabannin al'umma a yankin da lamarin ya faru sun ce rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum sama da 200 amma 'yan sanda a jihar ta Filato sun ce mutum 86 ne aka kashe.

Daruruwan mabiya addinin Kirista ne kuma su ka yi zanga-zanga a Jos, babban birnin jihar, suna kiran da hukumomi su dauki mataki kan abin ya faru.

Wasunsu kuma sun rinka daga kwalayen da ke kira ga Shugaban Amurka Donald Trump da ya kawo musu dauki.

A jawabin da ya yi a Jos din ranar Talata, Shugaba Buhari ya yi kira ga shugabannin al'umma su tallafa wa aikin wanzar da zaman lafiyar gwamnati wajen fadakar da mutanensu game da hakuri da zaman lafiya.

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kafa wani asusu na musamman domin sake gina kauyukan da aka lalata a hare-haren.

Ya ce gwamnatin jihar ta damu da irin makamai masu sarrafa kansu da aka yi amfani da su a hare-haren, lamarin da ya sa ta ke tunanin wannan hari ne na ta'addanci daga waje.

Hakkin mallakar hoto Nigerian Government
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin al'umma a jihar Filato
Hakkin mallakar hoto Nigerian Government
Image caption Gwamnan jihiar Kebbi da ministoci na coikin tawagar Buhari zuwa Filato

Sannan ya yi kira ga gwamnati ta mayar da martanin da ya dace kamar yadda aka mayar da martani ga Boko Haram.

Shugaba Buhari ya kuma saurari jawabi daga shugaban kungiyar Miyetti Allah ta jihar, Alhaji Nura Abdullahi, da kuma wakiliyar al'ummar Berom, Misis Florence Jambol, game da yadda za a tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al'ummomin.

Yadda lamarin ya auku

Wasu rahotanni sun ce fadan ya barke ne ranar Alhamis bayan da 'yan kabilar Berom suka farma wasu Fulani makiyaya, inda suka kashe biyar daga cikinsu.

Daga nan ne kuma aka ce wani hari na ramuwar gayya ya kai ga kisan wasu karin mutanen.

Yankin ya dade ya na fama da rikici tsakanin kabilun da ke rigima kan mallakar filaye.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da rikicin, sannan ya sha alwashin hukunta wadanda suke da hannu a lamarin.

Tun da farko an kashe gwamman mutane a wani rikici mai kama da wannan tsakanin Fulani da mafarauta a kasar Mali.

Tare hanya

Rahotanni dai na cewa mutanen yankin da ake rikicin suna tare hanya su na kashe mutanen da 'ba su ji ba, ba su gani ba,' wadanda yawancinsu matafiya ne da ke fitowa daga jihohin arewa maso gabas kamar su Bauchi da Gombe da Yobe, zuwa Abuja.

Su wayeFulani Makiyaya?

Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Images
Image caption Wani makiyayi yana bai wa dabbobinsa ruwa
  • Suna daga cikin ƙungiyar makiyaya mafi girma a duniya kuma ana samun su a yammaci da kuma yankin tsakiyar Afrika, daga Senegal zuwa jamhuriyar Tsakiyar Afrika
  • A Najeriya wasu sun cigaba da zama a matsayinsu na makiyaya, yayin da wasu suka koma birane
  • Fulani makiyaya suna yin akasarin rayuwarsu a daji ne, ba kamar mutanen da ke zama a cikin birane ba, kuma suna da alaƙa da waɗannan rikice-rikicen
  • Suna kiwon dabbobinsu a yankuna da dama, inda suke yawan yin rikici da al'ummomin da galibin aikinsu noma ne
  • Ana yawan dangantasu da ƙabilar Hausa, saboda tsawon lokacin da suka shafe suna zama tare
  • Fulani sun taka muhimmiyar rawa a ƙarni na 19 wajen farfaɗo da addinin Musulunci a Najeriya.

Me ke kawo rikicin?

Ana tunanin ce-ce-ku-ce a kan abubuwan more rayuwa kamar su gonaki da yankunan da ke da burtali da ruwa ne ke jawo rikici tsakanin makiyaya da kuma manoma.

Fulani makiyaya kan iya tafiya mai nisa tare da dabbobinsu domin nema musu abinci. Mafi yawan lokuta, suna daukar makamai domin kare dabbobin nasu.

Hakkin mallakar hoto other
Image caption Rikicin ya rutsa da matafiya da dama kamar wadannan da ba a tantance ko su wa ye ba

Suna yawan rikici da manoma wadanda ke yawan cewa suna lalata musu amfanin gona kuma ba sa kula da inda dabbobin nasu ke zuwa.

Fulanin na zargin cewa manoma waɗanda ke ƙoƙarin satar shanunsu - suna cewa suna ƙoƙarin kare kansu ne.

A da, rikicin a yankin tsakiyar Najeriya aka fi yi, inda kiristoci ƙabilar Birom da ke jihar Plateau suke kisan ramuwar gayya ga Musulmai da makiyaya.

Yadda sauyin yanayi ya ke shafar burtali ya sa Fulani makiyaya sun kara matsawa zuwa kudancin Najeriya domin neman ruwa da ciyawa.

Wannan ya ƙara faɗaɗa rikicin ta inda ake cigaba da fuskantar munanan tashe-tashen hankula a kudancin ƙasar, ana ƙara jin tsoron cewar rikicin zai yi barazana ga haɗin kan da dama ya ke tangal-tangal tsakanin ƙabilun Najeriya.