Kisan Filato: PDP na zaman makoki na kwana bakwai

Filato
Image caption Kiristoci sun yi zanga-zanga kan rikicin jihar Filato

Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta kaddamar da zaman makoki na kwanaki bakwai domin jimamin mutanen da aka kashe a jihar filato.

PDP ta bukaci a sassauto da tutarta a dukkanin ofisoshinta da ke fadin kasar har tsawon kwanaki bakwai da ta ayyana na zaman makokin kisan mutane sama da 200 a Filato.

A cikin sanarwar da kakakinta Kola Ologbondiyan ya aika wa manema labarai ciki har da BBC, jam'iyyar PDP ta ce "ya kamata al'ummar jihar Filato su yi amfani da 'yancinsu na 'yan kasa domin kai kara kotun duniya ta ICC kan gazawar gwamnati wajen kawo karshen yawan kashe-kashe a Najeirya."

Sai dai a lokacin da ya kai ziyarar jaje a jihar Filato, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kare sukarsa da 'yan adawa ke yi cewa gwamnatinsa ba ta yin komi a kashe-kashen rikicin makiyaya da manoma.

Shugaban ya ce ba a yi masa adalci game da yadda ake cewa ba ya daukar mataki kan Fulanin da ake zargi da kashe mutane saboda shi ma Bafulatani ne.

Ya ce : "Ya kamata a lura cewa 'yan Najeriya da yawa sun yarda cewar duk da kalubalen tsaron da ake fuskanta, wannan gwamnatin ta samu muhimman nasarori a bangaren tsaro."

A cikin sanarwar, jam'iyyar PDP babbar mai adawa da gwamnatin Buhari ta ce "hakkin gwamnati ne ta kare rayukan dukkanin 'yan Najeriya, ko da kuwa kabilar Birom ne ko Basange da Igbira da Tiv da Idoma da Hausa da Igbo da Fulani da Gbagyi da Yoruba da wata wata kabila a kasar."

Yadda lamarin ya auku

Wasu rahotanni sun ce fadan ya barke ne ranar Alhamis bayan da 'yan kabilar Berom suka farma wasu Fulani makiyaya, inda suka kashe biyar daga cikinsu.

Daga nan ne kuma aka ce wani hari na ramuwar gayya ya kai ga kisan wasu karin mutanen.

Yankin ya dade ya na fama da rikici tsakanin kabilun da ke rigima kan mallakar filaye.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da rikicin, sannan ya sha alwashin hukunta wadanda suke da hannu a lamarin.

Tun da farko an kashe gwamman mutane a wani rikici mai kama da wannan tsakanin Fulani da mafarauta a kasar Mali.

Image caption Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar jaje a Filato

Tare hanya

Rahotanni dai na cewa mutanen yankin da ake rikicin suna tare hanya suna kashe mutanen da 'ba su ji ba, ba su gani ba,' wadanda yawancinsu matafiya ne da ke fitowa daga jihohin arewa maso gabas kamar su Bauchi da Gombe da Yobe, zuwa Abuja.