An sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Sudan ta Kudu

Yerjejeniyar zaman lafiya a Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Irin wannan yunkuri da aka yi a baya ya ci tura

Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir da kuma abokin hamayyarsa, Riek Machar, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo karshen yakin basasar kasar da ya kai shekara biyar.

A karkashin yarjejeniyar za a tsagaita wuta cikin sa'o'i 72.

Yakin dai ya daidaita Sudan ta Kudu, inda dubban mutane su ka mutu kuma kusan mutum miliyan hudu - kashi daya cikin uku na al'ummar kasar- sun rasa muhallansu.

Kokarin dakile fadan a baya dai ya ci tura.

Rahotanni sun ce a karkashin yarjejeniyar ta baya-bayan nan, za a saki wasu fursinonin siyasa da ake tsare da su.

Mista Kiir da Mista Machar sun hadu ne a karon farko cikin kusan shekara biyu a makon da ya gabata.

Yarjejeniyar, wadda aka sanya wa hannu a babban birnin kasar Sudan, Khartoum, tana zuwa ne a lokacin da kasashe makwabta ke matsawa wajen ganin cewa an kawo karshen yakin.

Shugaban Uganda, Yoweri Museveni da kuma takwaransa na Sudan, Omar al-Bashir sun gana da Mista Machar da Mista Kiir gabanin zaman nasu.

Labarai masu alaka