Magidanci ya sayar da naman kare da sunan na akuya

Mozambique Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An zargin mutumin da kashe kare domin ya sayarwa jama'a

'Yan sanda a kasar Mozambique sun ce sun cafke wani mutum da aka kama shi yana yanka kare, wanda ake kyautata zaton cewa ya yi haka ne domin ya sayar da namansa a matsayin naman akuya.

Shugaban caji ofis din 'yan sanda dake unguwar Samora Machel ya ce an ba shi umarni daga sama a kan ya tura da jami'an 'yan sanda domin gudanar da bincike bayan da makwabta suka yi tsegumi kan batun wani mutum da ke fede kare.

"Na tura da mutane biyar zuwa wurin domin su gudanar da bincike. Sun je wurin kuma sun same shi yana aika-aikar."

Daga nan, sai 'yan sandan suka kama shi kuma suka kawo shi caji ofis.

Sai dai mutumin ya musanta zargin da ake yi a kan cewa yana son ya sayar da naman a kasuwa.

"Ba na sayar da nama a kasuwa. Na yanka dabar ce domin na ci. Ba ni da aniyyar sayar wa a kasuwa ko na ba matata ta yi girki da shi. Na so a ce ni kadai ne na dafa naman kuma na cinye abina ni kadai. Na ko yi haka ne daga wurin wadansu 'yan China," in ji shi .

A shekarun baya-baya nan, ana samun labarai mara dadin ji a lardin Tete - ciki har da masu cin naman mutum da amfani da sassan jikin zabiya da kuma yadda mutum 70 suka mutu bayan sun sha barasa mai guba.

Labarai masu alaka