‘Yan wasan Najeriya da ba 'za su sake zuwa kofin duniya ba’

Super Eagles

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Matasa ne suka mamaye tawagar Super Eagles na Najeriya a Rasha

Yayin da wasu 'yan wasan Super Eagles ke cewa za su haki gaba, wasu daga cikin 'yan wasan kuma damarsu ta karshe ke nan na wakiltar Najeriya a gasar cin kofin duniya.

Hukumar Fifa ta ce tawagar ta Najeriya ce mafi kankantar shekaru da suka tafi gasar cin kofin duniya a Rasha.

Mafi yawancin 'yan wasan da suka wakilci kasar suna tsakanin shekara 19 zuwa 26.

Mai tsaron ragar Najeriya Ozoho ne dan wasa mafi kankantar shekaru a tawagar Super Eagles inda ya ke da shekara 19.

Sai dai kuma akwai wadanda ko shakka babu ba za su sake zuwa gasar cin kofin duniya ba saboda wasu dalilai da suka hada da yawan shekaru.

Akwai kuma wasu daga cikin matasan da ake ganin ba za su yi karkon da za su samu damar sake wakiltar Najeriya a gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar 2022 ba.

Mun yi nazari game da makomar wasu 'yan wasan na Najeriya.

Matasan da ba su da tabbas

Asalin hoton, FIFA

Bayanan hoto,

A lokacin da za a yi Qatar 2022 Moses yana da shekara 31

Daga cikin wadanda ake ganin ba za su yi karkon sake wakiltar Najeriya ba a gasar cin kofin duniya, sun hada da Victor Moses da Ahmed Musa da Abdullahi Shehu da Nwankwo.

Dan wasan Chelsea Victor Moses wanda ya tafi Rasha yana da shekara 27, zai kasance kafin Qatar 2022 yana da shekara 31.

Makomarsa za ta dogara ne da rawar da zai taka nan gaba a wasannin kulub dinsa da kuma Najeriya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Musa shi ne dan kwallon da ya fi ci wa Najeriya kwallaye a gasar cin kofin duniya

Ahmed Musa da Abdullahi Shehu da Onazi dukkaninsu suna da shekara 25 a bana da suka wakilci Najeriya a Rasha amma kafin gasar cin kofin duniya a 2022, zai kasance 'yan wasan suna hararar 30.

Musa wanda ya zura kwallaye biyu da Najeriya ta doke Iceland, shi ne dan kwallon da ya fi ci wa kasar kwallaye a gasar kofin duniya.

Damar sake zuwa gasar cin kofin duniya ga Ahmed Musa da Abdullahi Shehu za ta dogara ne da rawar da suke taka wa a matakin kulub.

Wadanda shekarunsu ya ja

Babu shakka akwai wadanda shekarunsu suka ja, kuma daga dukkan alamu azama da kyan wasansu ma ya fara ja baya.

A don haka zai yi wuya a sake ganinsu a gasar kofin duniya a matsayin 'yan wasa.

John Mikel Obi

Asalin hoton, Getty Images

Kaftin din Super Eagles John Mikel Obi mai shekara 31 shi ne na biyu mafi tsufa a tawagar 'yan wasan da suka wakilci Najeriya a Rasha.

Mikel ya buga wa Najeriya wasa 85 tare da cin kwallaye 6. Ya lashe wa Najeriya kofin Afirka da tagulla a wasannin Olympic a Rio 2016.

Ana ganin nan da dan lokaci tsohon dan wasan na Chelsea zai sanar da yin ritaya daga buga wa Najeriya wasa.

Odion Ighalo

Asalin hoton, Getty Images

Ighalo da ke taka leda a kulub din Changchun Yatai na China zai yi wahala ya sake zuwa gasar cin kofin duniya.

Dan wasan na gaba yana shekara 29, ya wakilci Najeriya a Rasha, kuma kafin 2022 dan wasan ya haura 33.

Tsohon dan wasan na Watford ta Ingila ya ci wa Najeriya kwallaye 4 a wasanni 22 da ya bugawa kasar.

Leon Balogun

Asalin hoton, Getty Images

Karo na biyu ke nan da Balogon ya wakilci Najeriya a gasar cin kofin duniya.

Dan wasan na baya da ke taka leda a kungilar Mainz ta Jamus ya wakilci kasar a Rasha yana da shekara 30.

Balogun wanda aka haifa a Jamus, ya buga wa Najeriya wasa 22 amma ba tare da ya ci kwallo a raga ba.

Damarsa ta sake wakiltar Najeriya a gasar cin kofin duniya za ta dogara ne da rawar da zai ci gaba da taka wa a wasannin Najeriya da kuma kulub dinsa.

Ikechukwu Ezenwa

Asalin hoton, Getty Images

Zai yi wahala mai tsaron raga Ezenwa mai shekara 29 ya sake wakiltar Najeriya a gasar cin kofin duniya.

Ezenwa wanda ya taimakawa Najeriya a wasannin samun gurbi a Rasha, ya fara ganin makomarsa tun kafin fitar da Najeriya a gasar cin kofin duniya.

Ezenwa da ke tsaron ragar Ifeanyi Ubah ta Najeriya an ajiye shi ne a benci a dukkanin wasannin da Najeriya ta buga a Rasha.

Golan Deportivo La Coruna, Francis Ozoho mai shekara 19 ne aka ba dama a maimakon Ezenwa da Akpeyi.

Daniel Akpeyi

Asalin hoton, Getty Images

Mai tsaron ragar kungiyar Chippa United ta Afirka ta kudu Daniel Akpeyi mai shekara 32 shi ne mafi tsufa a tawagar Super Eagles a Rasha.

Duk da cewa Akpeyi ya samu damar zuwa Rasha amma har aka fitar da Najeriya yana benci.

Akpeyi wanda ya taba wakiltar Najeriya a matsayin mai tsaron raga a wasannin Olympics a 2016 yana da wahala ya sake zuwa gasar cin kofin duniya.