Rashin ruwa a BUK na yin cikas ga karatun Mata
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Rashin ruwa a BUK na yin cikas ga karatun Mata'

Dalibai mata a jami'ar Bayero da ke Kano sun shaida wa shirin Adikon Zamani girman matsalar ruwa da suke fuskanta.

Daliban sun ce rashin ruwan na haifar da cikas ga karatunsu.

Matan da ke kwana a jami'ar sun ce cikin sa'o'i uku kawai suke samun ruwa a rana. Sun ce matsalar na tilasta ma su kauracewa zuwa aji musamman lokacin da suke kokarin samun ruwan idan an kawo.

Sai dai hukumomin Jami'ar sun ce suna iya kokarinsu domin wadatar da daliban jami'ar da ruwa musamman a gidan kwana na mata.

Labarai masu alaka