Mayakan 'Boko Haram' sun kashe sojoji 10

Wani sojin kasar Nijar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Boko Haram ta dade tana farma sojojin Nijar a yankin Diffa

Wasu mahara da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kashe a kalla sojojin Nijar 10 a wani mummunan hari da suka kai.

Harin, wanda aka kai ranar Lahadi a yankin Diffa mai iyaka da Najeriya, ya yi sanadiyyar jikkata wasu karin sojin uku.

Hari ila yau wasu sojoji hudu sun bata sakamakon harin, wanda aka kai a wani sansaninsu da ke yankin.

Mai magana da yawun ma'aikatar tsaro ta kasar Abdoul-Aziz Toure, ya tabbatar da wannan adadi ga kamfanin dillancin labarai na AFP.

Rahotanni daga yankin sun ce akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutu ko suka ji rauni ya karu.

Boko Haram ta dade tana farma sojojin Nijar a yankin Diffa da saurtan yankunan da ke makwaftaka da Tafkin Chadi.

Wannan hari dai ya zo ne kusan wata guda bayan wani makamancinsa, inda aka kashe sojoji shida.

Hakan ne kuma ya kawo karshen watannin da aka shafe ana zaman lafiya a yankin, wanda ya dade a karkashin dokar ta-baci.