Lopez Obrador ya lashe zaben Mexico

Andres Manuel Lopez Obrador

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mr Lopez Obrador yana daga wa magoya bayansa hannu a lokacin da suke murnar nasararsa a Mexico City

Dan takarar masu ra'ayin kawo sauyi Andres Manuel Lopez Obrador ya kama hanyar lashe zaben shugaban kasar Mexico.

Hasashen hukuma ya nuna cewa ya samu sama da 53 cikin dari na kuri'un da aka kada - sama da ninki biyu na mutumin da ke bi masa.

Tuni dai sauran mutum uku da suka yi takara da shi suka mika wuya, inda suka ta ya shi murna.

Mr Lopes Obrador ya bayyana kansa a lokacin yakin neman zabe a matsayin mutum daya tilo da zai iya yakar cin hanci da rashawa da ya yi wa kasar katutu.

Bayan da hukumomi suka yi kiyasin cewa shi ya lashe zaben, Mr Obrador ya ce zai kawo muhimman sauye-sauye a kasar.

Da ya ke jawabi ga magoya bayansa, ya ce babban abin da zai sa a gaba shi ne yakar cin hanci da rashawa, wanda ya ce shi ne musabbabin haifar da rashin adalci da daidaito a tsakanin al'umma da kuma tashin hankalin da ya addabi kasar.

Dan siyasar mai shekara 65, ya shafe sama da shekara 10 yana gwagwarmayar kawo sauyi a fagen siyasar kasar. Kuma a yanzu al'ummar kasar sun ba shi dama.

Ya yi alkawarin samar da dama ga matasan kasar, sannan ya taimaki tsafaffi.

Duk da cewa bai yi cikakken bayani ba, amma a baya ya ayyana aniyarsa ta shirya kuri'ar raba-gardama domin shawo kan wasu muhimman abubuwa da ke raba kawunan 'yan kasar.

Ya kuma nuna alamun cewa zai iya tattaunawa da cimma yarjejeniya da Shugaba Donald Trump domin shawo kan kwarar bakin-haure ba bisa ka'ida ba zuwa Amurka, inda ita kuma Mexico za ta samu tallafin tattalin arziki.

Sai dai nasarar wadannan abubuwa za ta dogara ne kan rinjayen da zai samu a majalisar dokoki.

Shi ma Shugaba mai barin gado Enrique Pena Nieto ya taya shi murna, sannan ya yi alkawarin tabbatar da ganin an mika mulki cikin ruwan sanyi.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shugaba Donald Trump ya ce yana taya Mr Obrador murna.

Sannan ya kara da cewa yana fatan ganin sun yi aiki tare domin cimma wasu muhimman abubuwa da za su amfani Amurka da Mexico.