An gano 'yan gida daya rataye a wani gida da ke Delhi

Wata hanya a unguwat Burari a ranar1 ga watan yuli 2018
Image caption Mazauna unguwar sun ce iyalin na mu'amala sosai da sauran mutanen da ke Burari

'Yan sanda sun ce sun gano mutum 11 'yan gida daya a mace a wani gida da ke Delhi babban birnin kasar Indiya - inda 10 daga cikinsu sun mutu ne ta hanyar rataya.

Wata mata mai shekara 70 ce kadai aka gano kwance a kasa. Akasarin mamatan an rufe musu fuskokinsu da bakinsu, sannan kuma an daure mu su hannayensu ta baya.

Babu cikakken bayyanni game da mutuwarsu amma 'yan sanda sun ce suna zargin yiyuwar an musu kisan gilla.

Sai dai sun fitar da sanarwa da ke cewa sun gano shaida da ke nuna cewa iyalin na "ayuykan tsubbu".

Sanarwar ta ambato rubutun da aka yi a kan takarda da aka gano a cikin gidan wanda ke nuni da cewa "akwai alakar aikin tsubbu" dangane da mutuwar mamatan.

Har yanzu suna zaman jiran sakamakon binciken da za a yi kan gawawwakinsu da tambayoyin da ake yi wa makobta, da kuma nazari kan hotunan da kyamarorin tsaro suka dauka.

Wani jami'in dan sanda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: "ya yi sauri" a san abin da ya faru.

"Bincike ne da har yanzu ya ke gudana kuma ba mu yanke hukunci kan komai ba," in ji shi.

Iyalin sun yi shekara fiye da 20 da zama a yankin Burari na Delhi, duk da cewa asalinsu 'yan Rajasthan ne. Suna da shaguna biyu a kasan wani bene mai hawa uku.

Wani makwabcinsu ne ya gano gawawwakin mammatan lokacin da ya je shagonsu domin sayen madara da safiyar Lahadi.

Image caption Gurcharan Singh ne ya gano gawawwakin mamatan

"Lokacin da na shiga cikin shagon, dukkanin kofofi a bude suke kuma ga gawawwakin mutane na rataye a silin, kuma hannayensu a daure ta bayansu," kamar yadda Gurcharan Singh ya shaida wa sashen Hindi na BBC.

Ana kyautata zaton cewa a cikin mamatan akwai maza biyu wadanda 'yan uwa ne tare da matansu da 'ya'yansu da kuma wata tsohuwa. An dai gano karensu a raye.

Gawawwakin mamatan da aka gano ya sa mazauna unguwar sun dimauce, in ji sashen Hindi na BBC.

Mazauna unguwar da kuma danginsu sun ce iyali ne da ba su da matsala kuma suna kyakkyawar mu'mula da kowa.

Labarai masu alaka