An sake kashe mutum biyar kan 'jita-jitar WhatsApp' a Indiya

Dadarao Bhosale
Bayanan hoto,

Dadarao Bhosale daya ne daga cikin mutum biyar din da gungun mutanen ya kashe

Wani gungun mutane sun kashe mutum biyar a jihar Maharashtra da ke yammacin Indiya kan jita-jitar sace yara da ake yadawa a manhajar sada zumunta ta WhatsApp.

An kama mutum 12 game da kashe-kashen, wanda aka yi ranar Lahadin da ta gabata, kamar yadda 'yan sanda suka shaida wa shashen M arathi na BBC.

Wadanda lamarin ya rutsa da su dai makiyaya ne wadanda ke wucewa ta hanyar kauyen, in ji 'yan sanda.

Duk da kokarin da 'yan sanda suka yi na dakile su, ana ci gaba da samun irin wadannan kashe-kashen da ake yi bisa jita-jita.

'Yan sanda sun kafa dokar takaita zirga-zirga a kauyen yayin da ake ci gaba da zaman dar-dar bayan an tura karin jami'an tsaro wurin.

Sun ce mutane daga wannan al'ummar suna yawan wucewa ta kauyuka suna bara kuma suna hakan ne a lokacin da aka far musu.

An ga daya daga cikin mutanen yana magana da wata yarinya kuma wasu 'yan kauyen sun zargi mutanen kuma sun yi musu tambayoyi.

M. Ramkumar, wani babban jami'in 'yan sanda, ya shaida wa Pravin Thakre na sashen Marathi na BBC cewar : "Da yake mutanen kauyen ba su gamsu da amsoshinsu ba, sun kai mutanen cikin wani daki kuma suka fara dukansu da gora da duwatsu."

Ya ce mai yiwuwa ne jita-jitar da aka yi ta yadawa ta manhajar WhatsApp ta tunzara kisan.

Ya kara de cewa a lokacin da 'yan sanda suka isa wurin gungun mutanen ma sun far musu.

Bayanan hoto,

Mutane daga kabilar makiyayan sun gina gidaje na wucin-gadi a wani kauyen da ke kusa

Dada Bhuse, wani dan majalisa, ya shaida wa BBC cewa: "Wannan wani abu ne mai tayar da hankali da kuma rashin sa'a. Za mu dauki mataki mai tsauri kan wadanda ake zargi da kuma wadanda suka yada jita-jitar."

An bayyana sunayen mutane biyar din da lamarin ya rutsa kamar haka: Bharat Bhosale da Dadarao Bhosale da Raju Bhosale da Aganu Hingole da kuma Bharat Mawale.

Mace-macen da aka alakanta da jita-jitar WhatsApp

Watan Afrilu: Wani gungun mutane ya kashe wani mutum a kudancin jihar Tamil Nadu ta hanyar dukansa bayan an gan shi yana watangaririya a hanya.

Watan Mayu:

  • An kashe wata mata 'yar shekara 55 a Tamil Nadu domin ta bai wa yara alewa; 'yan sanda sun kama mutum 30
  • An kashe wani mutum a jihar kudanci ta Andhra Pradesh domin ya yi magana da harshen Hindi maimakon harshen yankin, Telugu
  • Wani gungun mutane ya kashe wani mutum a jihar Telangana mai makwabtaka a lokacin da yake shiga wani lambun mangoro
  • An kashe wani mutum a Telangana a lokacin da yake ziyartar wani kauye domin ganin 'yan uwansa
  • An daure tare da kashe wani mutum ta hanyar duka da sandan wasan kurket a birnin Bangalore da ke kudancin kasar
  • An kashe wata mata da ta sauya jinsinta a Hyderabad.

Watan Yuni:

  • An kashe mutum biyu a arewa maso gabashin Assam bayan sun tsayar da motarsu domin tambayar hanya
  • An kashe wata mai bara daga Rajasthan a Ahmadabad
  • An kashe mutum biyu a hare-hare biyu da gungun mutane suka kai Tripura
Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Mene ne hukumomi ke yi game da wannan?

Ana yada Jita-jitar sace yara a gundumomin Maharashtra. 'Yan sandan yankin sun raba takardun fadakarwa domin wayar da kan mutane game da jita-jita.

Jami'ai a wasu wuraren a kasar Indiya sun nemi mutane ka da su yarda da sakonnin da ke da alaka da sace yara.

"A lokacin da aka fara yada jita-jita a kafafen sada zumunta, ya kan dauki lokaci kafin a samu a dakile su gaba daya," in ji wani babban dan sanda a jihar Assam, Mukesh Agarwal, wanda ya zanta da wakilin sashen Hindi na BBC, Dilip Kumar Sharma, yana mai karawa da cewa 'yan sanda suna sa ido kan shafukan sada zumunta domin hana yada sakonnin.

A watan jiya, 'yan sanda a birnin Hyderabad da ke kudancin kasar sun yi maci da mutanen gari da lasifika suna cewa "kada ku yarda da jita-jita".

A jihar Tamil Nadu, inda aka bayar da rahoton irin wadannan tashe-tashen hankulan a cikin a 'yan watannin nan, hukumomi sun fara kamfe na wayar da kan jama'a game da jita-jita.

A wasu jihohin kudancin kasar irin su Karnataka, 'yan sanda sun kafa ofishin shawo kan shafukan sada zumunta inda suke sa ido kan sakonnin da ake wallafawa da sakonnin da ake yayatawa da kuma sakonnin bidiyo.

'Yan sanda a jihar Telangana sun yi gargadi kuma sun kama mutanen da suka yayata sakonnin bidiyo na karya.