An gano wata mata da ranta a firij din mutuware

taswira

Wata mata 'yar Afirka ta Kudu tana murmurewa a asibiti bayan an gano tana da rai a cikin firij din mutuware.

An kai matar mutuwaren Carletonville, a lardin Gauteng, bayan ma'aikatan jinya sun bayyana cewa ta mutu sanadiyyar hatsarin mota.

Kamfanin motar daukar marasa lafiya na Distress Alert ya ce ba ta nuna "wata alamar tana da rai ba," in ji rahotanni daga kamfanin jaridar TimesLive ta intanet na Afirka ta Kudu.

Amma yayin da wani ma'aikacin mutuware ya dawo ya duba gawar a cikin firij, sai ya tarar da matar tana numfashi.

Wani jami'i ya tabbatar wa BBC cewa ana kula da matar a asibitin, sai dai ba a ambaci sunanta ba.

An gudanar da binciken kan lamarin, amma shugaban kamfanin motocin daukar marasa lafiya na Distress Alert Gerrit Bradnick, ya ce babu "tabbacin rashin kulawa" a madadin kamfaninsa.

"Wannan abun ba wai ya faru ba ne don rashin kulawa ko rashin iyawar ma'aikatan jiyarmu ba ne," ya fada wa TimesLive.

Mr Bradnick ya fada wa TimesSelect cewa matar na daya daga cikin mutane da yawa da suka rasu a hatsarin motar, inda mutum biyu suka rasa rayukansu a ranar Lahadi 24 ga watan Yuni.

Wannan ba shi ne karon farko da aka gano wani da ransa bayan da aka yi tsammanin ya mutu ba a shekarar nan.

A watan Janairu wani mutum a kurkuku a yankin Asturias na Spaniya ya sake farfadowa sannu a hankali, sa'o'i da yawa kafin a fara yin bincike.

Likitoci uku suka tabbatar da mutuwarsa.

A Afirka Ta Kudu ma ba wannan ne karo na farko da wannan abu ya faru ba. Shekaru bakwai da suka wuce, wani mutum mai shekara 50 ya farka da kururuwa a cikin matuware ta Eastern Cape.

Haka ma a shekarar 2016 bayan an kai wani mutum da ya yi hatsarin mota mutuware daga KwaZulu Natal, an bayyana cewa ya mutu, amma kwatsam washe gari sai aka ga yana numfashi.

Amma bayan sa'a biyar da gano hakan sai kuma ya mutu.