Wani ya kai hari a wurin liyafar yara a Amurka

Timmy Kinner, Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana tuhumar Timmy Kinner, wani mazaunin Los Angeles da aika-aikar

Wani mutum ya raunata mutane tara a harin da ya kai da wuka a wata liyafa da aka shirya wa yara, wadanda suka halarci bikin zagayowar shekarar haihuwar wata yarinya a Boise, da ke Idaho, in ji 'yan sandan Amurka.

Sun yi amannar cewa harin da aka kai ranar Asabar a wani wuri da 'yan gudun hijira suke mafaka, "ramuwar gayya" ce ta haddasa shi, bayan da aka nemi mutumin da ake zargi a kan ya bar wurin, kwana daya kafin a gudanar da bikin.

Yara shida - masu shekaru uku zuwa 12 - na cikin wadanda aka raunata. Galibin 'yan gudun hijirar da ke wurin daga kasashen Habasha da Iraki da kuma Syria ne suka fito.

An bayyana sunan mutumin da ake tuhuma da Timmy Kinner, mazaunin birnin Los Angeles.

Ana tuhumar Mr Kinner, mai shekara 0, da cin zarafi tare da raunata yara.

Shugaban hukumar 'yan sandan Boise, William Bones, ya fada wa 'yan jarida cewa mutumin na zama ne tare da wani abokinsa a ginin amma an koreshi a ranar Juma'a.

Ya koma wurin washegari domin ya "rama " abin da aka yi masa , inda ya kai wa mutane hari a bikin zagayowar ranar haihuwar wata 'yar shekara uku ,in ji Mr Bones.

"Bincike ya nuna cewa an kai hari ne kan wadanda suke zama a wurin ba wai wadanda suka san mutumin da ke zargi ba," in ji shugaban 'yan sandan.

Labarai masu alaka

Karin bayani