Yadda wata shuka ta inganta rayuwar mata a Zanzibar

Image caption Wasu mata a Zanziba

Wani tsiron teku da ake kira Seaweed da Turanci na ci gaba da samun karbuwa a wurin mutane, ana amfani da shi a cikin man goge baki da magani da kuma sabulun wanke gashi.

A Zanzibar, harka ce da ke samun tagomashi, kuma mata ne suka fi nomawa, kuma ya rage gibin da ke tsakanin maza da mata wajen kula da iyali.

Wasu mata da ke rike da igiya da sanduna a ka na tafiya da asuba domin zuwa bakin teku inda za su shuka bado a gabar teku.

Suna bangaren teku da ruwa ya tsaya a gwiwarsu, kuma sun tura sandarsu a cikin kasan tekun. Ana hada kananan tsirran ruwan teku tare da igiya kuma za a shuka su a tsakanin sandunan da aka kafa a cikin teku.

A cikin makoni shida irin da aka shuka za su tsiro kuma a girbe. Za a yi amfani da wasu a cikin girki sai dai galibi za a busar da su domin a sayar wa wani dillali wanda zai tura zuwa kasashen waje.

Matan kan yi wa juna shagube da kuma gulma.

A lokacin da aka shigo da noman Seaweed a farkon shekarun 1990, maza ba su dauki aikin da muhimanci ba. Sun fi son kamun kifi ko aiki a kamfanonin yawon bude ido. Sai dai akwai wasu da ba sa son matansu su yi aiki a gona.

Mohamed Mzale, shi ne shugaban al'ummar kauyen Paje da ke gabashi, kuma ya fito baro-baro wajen bayyana ra'ayinsa.

"Na rika tsamanin cewa harkar kasuwanci ta Seawood wata dabara ce ta kayyade iyali, saboda yawan sa'o'in da mata suke yi a bakin teku a kuma aikace-aikacen gida kan su su gaji gaya - har su kasance ba su da lokacin saduwa da mazajensu balle a samu karuwa."

Da farko Mohamed ya ki amince wa matarsa ta farko zuwa bakin teku da sauran mata. "Ta daina walwala kuma ta rika kuka," in ji shi. Daga bisani ya amince.

Noman Seawood ya karfafa wa mata ta yadda ba sai sun jira mazansu ba wajen kula da iyali a tsibirin da musulmi suke da rinjaye.

A baya matan kauyen na fita daga gidjensu domin halartar jana'iza ko daurin aure ko kuma dubiya.

Yadda ake kebesu a bayyane yake a tsarin gina gidajesu - akwai gidaje da dama masu kujerun da aka yi da siminti a wajen gida, wadanda suke bai wa maza damar karbar baki a waje ba tare da sun shiga cikin gida ba.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption An kiran kujerun bazaras a Zanzibar

"Da farko wasu mazan sun rika barazanar sakin matansu idan suka fita daga gidajensu domin shuka tSeawood a teku," in ji Flower Msuya, kwarariya kan halittun ruwa.

"Sai dai da su ka ga cewa matan na samun kudi daga harkar, sannu a hankali sun rugumi harkar sosai."

Mata sun rika zuwa kasuwa tare da yin baluguro a cikin motocin safa-safa domin zuwa birnin a maimakon barin mazajesunsu da cefane.

A cikin kankanin lokaci iyalai da dama sun sami dama da karfin sayen littattafan makaranta da kayan makaranta da kujeru da abinci mai gina jiki, kuma sun sauya saman gidajensu da kwano a maimakon jinka.

Image caption Safia Mohamed, da danta wanda ya ke kan babur din da ta saya masa

Safia Mohamed, mai noman seawood ce a kauyen Bweleo da ke kudu maso yammacin Zanzibar, kuma ta inganta rayuwarta.

Tana da shagon sayar da sabulun da aka hada da seawood da zumar da ake shafawa a burodi wato 'Jam' da kuma kayan girki domin kara dandano mai dadi.

Daga cikin ribar da ta samu ta sayawa 'ya'yanta maza jirgin ruwan kamun kifi da babur kuma ta gina katafaren gida.

"Yarana hudu, kuma tun shekarar 1985 na yi aure kuma ni kadai ce a wurin mijina," in ji ta.

Safia ta fadawa BBC cewa za ta amince idan mijinta ya ce zai yi mata kishiya saboda haka addinin musulunci ya tanada. Sai dai ta ce ba za ta amince wa amaryar ta zauna a cikin gidanta ba.

Karin bayanni

Kusan kashi 50 cikin 100 na matan da ke tsibirin mazajensu sun sake su saboda sun kada kuri'a a zaben shekarar 2015, ko kuma sun kada kuri'a ga 'yan takarar da mazajensu ba su amince da su ba.

Kotunan shari'ah guda goma da ake da su a Zanzibar da kuma makobciya Pemba suke sauraran kararrakin ma'aurata.

A bisa ka'ida ko wanne daga cikinsu na da hakkin neman rabuwa, ko da yake a al'ada miji ne yake neman rabuwa da matarsa.

Image caption Mwanaisha Makame tana saka

Kamar Safia 'yar kasuwa, Mwanaisha Makame ita ma ta yi amfani da kudin da ta samu daga noman seawood wajen inganta rayuwarta.

Ta nuna wa wakiliyar BBC wani bangare na ginin da take yi da ta ce za ta koma idan aurenta ya mutu.

"Babu tabbas a zamantakewar aure a Zanzibar," ta yi dariya. " Idan mijinmu yana da wata da yake so, to soyayyar za ta iya sa shi ya fita daga cikin hayyacinsa har ya kai ga rabuwa da ke."

Image caption Mwanaisha's T-shirt reads: Seaweed is food and seaweed is a job

Sai dai matan na fuskantar wata matsala kuma - wato ta sauyin yanayi.

A tsibirin Pemba ne ake shuka akasarin seawood, sai dai wuri ne mai duwatsu kuma ruwan da ke karuwa a cikin teku ba ya yi masa illa.

Sai dai an dakatar da shuka seaweed din a garin Paje tun a shekarar 2011.

Amma sannu a hankali ana komawa bakin teku domin shuka shi, ko da yake irin da ba shi da inganci sosai ne ake shuka wa wanda ba shi da sinadrin carrageenan - wanda ake amfani da shi a cikin abinci, da kayan kwalliya da kuma magunguna.

A sakamakon haka harkar kasuwanci na fuskantar koma baya.

Image caption Mata masu noman seawood

Reziki, wadda makobciyar Mwanaisha ce, na matukar bukatar kudi saboda tana da yara bakwai amma yanzu tana sayar da Samosa ne.

Sauran matan da suke shuka seaweed a yanzu sun rungumi sana'ar hannu inda suke sayar da kayayyakin da suka yi ga masu yawon bude ido.

Kuma a bayyane take cewa aikin da suka yi a wajen gidajensu na cikin abubuwan masu alfanu na tsiren ruwan teku na seaweed.