Yar shekara 3 da aka shirya wa liyafa ta mutu a Idaho

Timmy Kinner, mutumim da ake zargi da kai hari da wuka a Boise da ke, Idaho Hakkin mallakar hoto Reuters

'Yan sanda a Amurka sun ce yar shekara uku da aka shirya wa liyafar zagayowar ranar haihuwarta ta mutu a ranar Litinin sakamakon raunukan da ta samu , bayan harin da wani ya kai da wuka , inda ya raunata mutum 9 a Boise, da ke Idaho

Sun yi amannar cewa harin da aka kai a ranar Asabar a wani wuri da 'yan gudun hijira suke samun mafaka, "ramuwar gayya" ce ta haddasa shi, bayan da aka nemi mutumin da ake zargi a kan ya bar wurin, kwana daya kafin a gudanar da bikin saboda ya nuna dabiun da basu dace ba

Har yanzu akwai mutum bakwai a asibiti , inda wasu daga cikinsu sun sami "munanan raunuka "

An bayyana sunan mutumin da ake tuhuma da Timmy Kinner, dan kasar Amurka .

Dukkanin mutum tara da aka kai wa hari a ranar Asabar 'yan gudun hijira ne da suka fito daga daga Habasha da Iraki da kuma Syria

Yara shida - masu shekaru uku zuwa 12 - na cikin wadanda aka raunata, ciki har da 'yar shekara ukkun da aka shirya wa liyafa wadda ta rasu a Utah bayan da aka kai ta wani asibitin da ke can domin a yi mata magani '

'Yan sanda sun ce an salami yaro daya daga asibiti bayan da ya gama karbar magani .

Shugaban 'yan sanda William Bones ya ce : "Wannan hari ne da aka kai kan wadanda ba zasu iya kare kansu ba : yaranmu ."

An gurfanar da Mr Kinner, mai shekara 30 gaban kotu , kan tuhumar kissan gilla da kuma raunata yara .

''Yan sanda sun ce Mr Kinner, ya aikata laifi a wasu jihohin Amurka kuma yanzu suna tsare da shi ba tare da karbar beli ba.

Labarai masu alaka