Tambuwal ya ba dan wasan Super Eagles kyautar gida

Dan wasan Super Eagles Hakkin mallakar hoto Twitter/Abdullahi Shehu
Image caption Shehu Abdullahi yana daya daga cikin 'yan wasan da suka wakilci Najeriya a gasar cin kofin duniya a Rasha

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tabuwal ya bai wa dan wasan Najeriya Shehu Abdullahi kyautar gida da fili da kujerar hajji da kuma kyautar kudi a matsayin tallafi ga gidauniyarsa, kamar yadda dan wasan ya bayyana.

Dan wasan, wanda yake cikin tawagar da ta wakilci kasar a gasar cin kofin duniya a Rasha, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Litinin.

Mai taimakawa gwamman jihar kan yada labarai Abubakar Shekara ya tabbatarwa wa BBC labarin, kuma ya ce an ba shi filin ne don ya kafa wata Gidauniyar Wasanni wadda za a sanya wa sunan dan wasan.

Shehu Abdullahi wanda dan asalin jihar Sakkwato ne ya yaba wa gwamnan.

Kasar Argentina ce ta cire Najeriya daga gasar cin kofin duniya a matakin rukuni, bayan ta doke ta da ci 2-1.

Hakkin mallakar hoto Twitter/@Official Shehu
Image caption Dan wasan ya kai ziyara fadar gwamnan jihar da ke Sakkwato
Hakkin mallakar hoto Twitter/@Official Shehu
Image caption Shehu Abdullahi wanda dan asalin jihar Sakkwato ne ya yaba wa gwamnan

Labarai masu alaka