'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda 'bakwai' a Abuja

Nigeria Police Hakkin mallakar hoto AUDU MARTE
Image caption Wadansu 'yan sanda sun yi zanga-zanga a Maiduguri ranar Litinin

Wadansu 'yan bindiga sun kashe 'yan sanda "bakwai" a Abuja, babban birnin Najeriya a ranar Talata.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan birnin DSP Anjuguri Manzah ya tabbatar da faruwar al'amarin a wata sanarwa daya aike wa BBC.

Sai dai bai yi karin haske ba game da adadin jami'ansu da suka rasa ransu sanadiyyar abin da ya kira "bata-kashi", amma ya ce an fara gudanar da bincike don gano maharan.

Rahotanni sun ce al'amarin ya faru ne a mahadar unguwar Galadimawa da ke kan hanyar filin jirgin saman Abuja.

'Yan bindigar sun harbe 'yan sanda ne lokacin da suke wani shingen bincike, inda 'yan bindigar suka rika yin harbi daga cikin wata mota da suke tukawa, a cewar rahotanni.

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka