Tsohon Firaministan Malaysia na fuskantar tuhuma

Mista Najib Razak bai nuna damuwa ba a lokacin da ya isa kotu a Kuala Lumpur Hakkin mallakar hoto AFP/getty
Image caption Mista Najib Razak bai nuna damuwa ba a lokacin da ya isa kotu a Kuala Lumpur

An soma tuhumar tsohon firaministan Malaysia, Najib Razak, da cin amana da rashawa a wata Babbar kotu da ke Kuala Lumpur.

Tuhume-tuhumen na da alaka da batan bilyoyin daloli daga asusun gwamnati a lokacin da yake karagar mulki.

Wakilin BBC ya ce cikin yanayin nuna rashin damuwa Mista Najib ya isa kotun Kaula Lumpur, daruruwan mutane sun taru domin nuna masa goyon baya da gaisuwa, wasu kuma na son ganin yadda tsohon firaministan ya isa kotun.

Mista Najib dai na fuskantar tuhume-tuhume 4 daya hada da mafani da matsayinsa wajen aikata rashawa, sai dai tsohon firaministan ya musanta dukkanin zarge-zargen.

A jiya Talata aka cafke Mista Najib mai shekara 64 a gidansa -- kasa da wata 2 da rashin nasara a zaben kasar da ya sha kaye a hannu tsohon mai-gidansa Mahathir Mohamed.