'Yan sabuwar PDP sun kafa sabuwar APC'

Tutar APC Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tsoffin 'yan sabuwar PDP da suka hada da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da kuma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun kirkiro wani bangare a cikin jam'iyya mai mulkin Najeriya APC, da sunan Reformed APC, ko rAPC.

An bayyana hakan ne bayan wasu jiga-jigan 'yan APC da suka hada da 'yan bangaren sabuwar PDP sun yi wani taro a Abuja ranar Laraba, inda suka bayyana Injiniya Buba Galadima a matsayin shugabansu.

Sai dai duka shugabannin majalisar dokokin kasar da kuma Sanata Kwankwaso ba su halarci taron ba.

Kodayake shugabannin taron, sun ce da yawunsu aka dauki wannan mataki.

Sai dai uwar jam'iyyar APC ba ta ce komai ba tukuna game da batun.

Har ila yau sun ce sun yi ikirarin cewa su ne tabbatacciyar jam'iyyar APC.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Shugaban sabuwar APC Injiniya Buba Galadima
  • Latsa alamar lasifika da ke sama don sauraron hirar da muka yi da shugaban sabuwar jam'iyyar.

A karshen makon jiya ne Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa yanzu shi ba dan kowace jam'iyya ba ne.

Hakazalika ya yi ikirarin zai iya doke Shugaba Buhari idan jam'iyyar PDP ta tsayar da shi a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019.

An dade ana takun-saka tsakanin wadanda suka shigo jam'iyyar kafin zaben 2015 da ake kira 'yan sabuwar PDP da kuma bangaren gwamnatin APC.

'Yan sabuwar PDP sun yi zargin cewa ba a damawa da su a gwamnatin APC tare da barazanar daukar mataki idan har ba a biya bukatunsu ba.

Sannan a wani bangaren kuma ana tafiya ne da sunan jam'iyya daya amma akwai masu hamayya da juna a APC musamman a jihohi da dama da jam'iyyar ke mulki.

An samu bangarorin APC da suka gudanar da nasu zaben shugabannin jam'iyyar na daban a matakin mazabu da kananan hukumomi da kuma jiha.

Bangaren Kwankwasiyya na daga cikin bangarorin APC da suka gudanar da nasu zaben shugabannin jam'iyya a matakin mazabu da kananan hukumomi da kuma jiha.

Sannan tsohon gwamnan na Kano kuma sanata a APC ya kauracewa zaben shugabannin jam'iyyar na kasa da aka gudanar a Abuja.

Kwankwaso ya ce zuwansa babban taron na APC na iya haifar da abin kunya da rikici.

Masharhanta siyasa na ganin rigingimun APC da ta ke fama da su na iya yi wa jam'iyyar illa sosai a zaben 2019.