Malam Adamu Ciroma ya rasu, yana da shekara 83

adamu chiroma Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption An haife shi a watan Nuwambar 1934 a garin Potiskum

An yi jana'izar marigayi Malam Adamu Ciroma a masallacin Al Noor da ke Abuja.

Kanin marigayin Abu Ladisa ya ce, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya rasu ne a ranar Alhamis da rana a Abuja, bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Marigayin wanda ya taba neman takarar shugabancin kasar, ya taba rike mukamin ministan kudin kasar a tsakanin shekararun 1999 zuwa 2003.

Jama'a musamman manyan 'yan siyasar kasar suna ci gaba da mika sakon ta'aziyyarsu ga iyalan marigayin.

Hakkin mallakar hoto Twitter/@SPNigeria
Image caption An yi wa marigarin sallar jana'iza ne a masallacin Al Noor da ke Abuja ranar Alhamis

Shugaban Majalisar Dattawa kasar Bukola Saraki ya bayyana mutuwarsa da wani babban rashi ga kasar, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Hakazalika shi ma tsohon mataimakin shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar, ya wallafa sakon ta'aziyyarsa ta shafinsa na Twitter.

"Na yi bakin cikin samun labarin rasuwar Malam Adamu Ciroma. Shawarwarin da na rika samu daga wurinsa sun taimaka mini wajen kai wa ga matsayin da na samu kai a yanzu," in ji Atiku Abubakar.

Wane ne Adamu Ciroma?

  • Dan asalin garin Potiskum ne da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya
  • An haife shi a watan Nuwambar 1934
  • Ya tsaya takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar NPN a shekarar 1979
  • Ya taba zama minista sau uku a Najeriya da suka hada da minsitan Masana'antu da na Harkar Gona da na Kudi
  • Ya taba zama gwamnan babban bankin Najeriya, CBN
  • Yana daya daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar PDP
  • Shi ne ya jagorancin yakin neman zaben tsohon shugaba Olusegun Obasanjo a shekarar 2003.

Labarai masu alaka