Indiya: Za a inganta tsafta a cikin jiragen kasa

Indian Trains Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jiragen kasa a Indiya na daukan fiye da mutum miliyan 24 a kowace rana

An dade ana yaba ma jiragen kasa na Indiya saboda yadda jiragen ke safarar miliyoyin mutane a kowace rana, amma a yanzu matafiya na sukar yadda aka bari komai ke lalacewa.

A bara, an bayyana abincin da ake ba matafiya a cikin jiragen kasa a matsayin wanda kare ma ba ya ci ba.

A watan Mayu hankula sun tashi bayan wani abin kyama da ya hada masai da ruwan shayin da ake ba matafiya.

Amma kamfanin na wani sabon kokari domin dawo da martabar wannan muhimmin bangare na sufuri.

Fiye da mutum miliyan 24 ke bin jiragen kasa a Indiya a kowace rana, amma wasu jerin abubuwan takaici sun sa yawancin matafiya daina cin abincin da ake sayarwa a cikin jiragen kasa.

A bara, hukumar gwamnatin Indiya mai kula da cin hanci da rashawa ta gano cewa bai kamaci dan Adam ya ci abincin da ake hadawa a cikin jiragen kasa ba.

A wani rahoto mai kakkausar suka da hukumar ta fitar, ta ce yawancin abincin rubabbe ne kuma tuni lokacin amfani da shi ya wuce.

Matafiya dai sun dade sun kokawa da yadda akan ci karo da kwari a cikin abinci, kuma beraye da kyankayasai sun mamaye dakunan dafa abinci a dukkan jiragen kasa masu jigilar al'umma.

A watan Mayu ne dai komai ya kai karshe bayan da aka nuna bidiyon wani ma'aikacin jirgin kasa yana amfani da ruwan masai wajen hada shayin da yake ba matafiya.

Amma yanzu kamfanin Indiyan Railways ya lashi takobin inganta tsafta da kiwon lafiya - a wani sabon yunkuri da yake yi na dawo da martabar tafiya ta jirgin kasa a kasar - ta hanyar nuna ma matafiya yadda ake hada abinci a cikin jiragen kasa kai tsaye ta hanyar intanet.