Kun san yadda yin kuskure zai amfanar da ku?

Woman putting her hand on her eyes, as if she's regretting having made a mistake

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

kaico! Ki yarda...dukkanmu mun tsani yin kuskure

Daga yadda aka gano Amurka da subutar baki da kuma kura-kurai masu daukaka... ba dole ba ne yin kuskure ya zama abu mafi muni ba.

A gaskiya, kurakurai na iya zama abubuwa masu amfani.

Ko kuma a kalla, irin tunanin da suke yi ke nan a shirin 'Something Understood' - wani shirin BBC ne na kwarin gwiwa da yake nazari kan abubuwan da ke biyo bayan kura-kurai...

Da kuma yadda za mu amfana da su.

1.Yadda muke koyon darasi ke nan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mu gani... wanne kuskure ne aka samu? Sau da yawa za mu iya koyo daga kurakuranmu

Dukkanin mu mun ji tsohuwar maganar nan da ke cewa "kana koyo daga kurakuranka".

Kuma gaskiya ne - jarraba abu da kuskure wani muhimmin bangare ne na yadda kwakwalenmu da kuma kwarewarmu ke inganta.

Yi tunanin jaririn da ke koyon tafiya, mai wasan motsa jiki a lokacin da yake neman kwarewa, ko kuma wani mai yin kek a lokacin da yake yin kek daya tilo sau 20 domin ya burge alkalin gasa.

Masu ilimin halayyar dan Adam a jami'ar jihar Michigan sun nuna mana cewar in har mutum na son koyon darasi daga kurakuransa, zai fi cimma burinsa in yana da imanin cewar ilimi abu ne da zai iya inganta idan aka yi aiki a kai.

A wani binciken da suka yi kan wasu yara 123, sun lura cewar wadanda suka yi tunanin cewar ilimi ba abu ne mai tsayawa a wuri daya ba sun fi mayar da hankali kan kurakuransu, kuma saboda haka suna koyon karin darasi.

2. Zai iya yin tasiri mai kyau da ba a tsammani

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Daga "danko mara kyau" zuwa harkar miliyoyi -takardar sako mai danko ( "Post-It notes" a Ingilishi) ta samu ne ta hanyar kuskuren wani mai kirkira

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ba ko wane kuskure ne yake da amfani ba, amma masu yawa a cikinsu na da shi.

Christopher Columbus ya hau jirgin ruwa domin samun wata sabuwar hanyar ruwa ta zuwa Asiya - domin tabbatar da cewa da gaske duniya a zagaye ta ke kamar kwallo- amma maimakon haka sai ya yi kicibis da Amurka.

A wani mataki na daban, kurakuran da masu kirkira suka yi sun kai ga muhimman sabbin abubuwa, ciki har da na'urar dumama abinci da na'urar inganta aikin zuciya ("wato pacemaker"a Ingilishi).

Idan ba don karamin kuskuren da masanin kimiyyar Scotland, Alexander Fleming ya yi cikin shekarar 1928, da shekara 90 da suka gabata sun bambanta.

Fleming ya gano maganin kwayar cuta penicillin bayan wani gilashin gwajin da ya bari a waje da ya tafi hutu ya gurbata.

Kafin ya wanke shi, ya lura da wani abu da ya fita daban a cikinsa - inda hunhuna ta fito, amma kwayoyi ba su fito ba.

Wannan ba hunhuna kawai ba ce, sinadarin 'noatum' ne na penicillium.

Abin da ya biyo baya shi ne kirkiro tare da hada penicillin a matsayin wata hanya ta yakar cututtukan kwayoyin cuta.

Kun ga kuskure da wauta da ya ceci miliyoyin rayuka.

3. Yana koya mana darasi game da kawunanmu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ji nake kamar in mutu a nan domin kunya... Kura-kurai ka iya sa mutum ya ji kunya

Oscar Wilde ya rubuta cewar "kwarewa ce sunan da kowa ke saka wa kurakuransa".

Azanci a maganarsa ya shafi wani muhimmin abu - bata abubuwa wani muhimmin bangare ne na koyi game da kanmu da kuma rayuwarmu.

Ka fadi a wata babbar jarrabawa, sannan za ka san yadda za ka yi da bacin rai.

Ka ture wani abun tarihi na gidanku, sannan za ka san ko za ka iya magana a wani yanayi na kunya.

Ko kuma, in kai wani mai 'wa'azin karni na 19 William Miller ne, ka gamsar da mutane bisa kuskure cewar karshen duniya ya zo kusa, za ka gane in har kana da zuciyar amsa kuskuren da ka yi.

Da safiyar ranar 22 ga watan Oktobar shekarar 1844, Miller ya fuskanci dubban mabiya wadanda hankalinsu ya tashi, bayan dawowar Annabi Isa da ya ce zai auku, ya gaza aukuwa.

Duk da bacin ran da aka nuna da kuma dariyar da aka yi masa, Miller ya tunkari kuskurensa: "Mun tsammanci zuwan Almasihu a wannan lokacin. A yanzu, idan muka ce ba mu yi kuskure ba, ba za mu yi wa kawunanmu adalci ba. Ka da mu taba jin kunyar amsa kurakuranmu."

Sauya wannan mazuran!

4. Zai iya ba mu 'yancin bin abubuwan da muke so

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mance! Kasancewa cikin tsoron yin kura-kurai ka iya kasancewa rashi

Theodore Roosevelt ya ce: "Mutumin da ba ya yin kuskure shi ne wanda bai taba yin komai ba."

Tsoron kuskure ka iya hana mu yin sabbin abubuwa, daukar kurakurai a matsayin abubuwa na yau da kullum ka iya tasiri na akasin haka - ba mu da 'yancin bin abubuwan da muke son cimma ba tare da wata iyaka ba.

5. Zai iya taimaka mana wajen fitar da abin da ya kamata mu mayar da hankali a kai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sanin cewa "abu mafi muni" ya riga ya faru na taimaka miki ki mayar da hankali, in ji JK Rowling

A lokacin da ta kai 'yan shekara 25, JK Rowling ta ce ta riga ta yi kuskure mai yawa sosai.

Aurenta ya mutu, ita da 'yarta na rayuwa cikin talauci - wace dama take da ita ta yin nasara a matsayinta na marubuciya?

A wani jawabin da ta yi wa dalibai masu kammala karatun digiri a shekarar 2008, a Jami'ar Harvard, ta ce, "Na daina yaudarar kaina cewar ni wata ce maimakon ni kaina, sannan tara karfi na wajen kammala abin da na fi damuwa da shi."

"Na 'yantu," in ji ta, "domin abin da na fi tsoro ya faru, kuma ban mutu ba, kuma ina da 'ya da nake matukar so, kuma ina da tsohuwar na'urar rubutu (typewriter) da kuma wata babbar dabara."

Wannan dai ta taimaka wa marubuciyar Harry Potter wadda ita ce daya daga cikin marubutan da aka fi sani a duniya kuma wadda ta fi kudi.

6. Zai iya ba mu wani abu da za mu iya dariya a kai ... daga baya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

In ka samu lokaci, za ka iya rinka ganin ababen ban dariya a ko wanne yanayi

Daga "A Comedy of Errors" na Shakespeare zuwa littafin John Cleese mai suna "Fawlty Towers", da yawa daga cikin littatafan barkwancinmu sun ginu ne a kan kurakurai da kuma rashin fahimta.

Idan aka dan samu lokaci, kurakurai ka iya bayar da dariya sosai.

Saboda haka, duk da cewa za ka iya fargaba game da rufe makullin gidanka cikin gida yayin da kake sanye da rigar barci da safiyar yau, akwai yiwuwar cewar za ka fara dariya game da shi nan ba da jimawa ba.