Buhari ya ayyana dokar ta-baci kan yaki da cin-hanci

Buhari Hakkin mallakar hoto Facebook/Nigeria Presidency
Image caption Shugaban ya sanya hannu a dokar ne a ranar Alhamis

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ayyana dokar ta-baci kan yaki da cin hanci da rashawa a fadin kasar a ranar Alhamis.

Ya bayyana matakin ne lokacin da ya sanya hannun kan wani sabon umarni wanda da zai ba da damar kwace dukiyar da ake zargin ta sace ce.

Har ila yau ya ce umarnin zai shawo kan haramtattun harkoki ta hanyar sayar da dukiyar da aka samu daga wata badakala don magance cin hanci da miyagun illolinsa.

Ya ce daga alkalluman da ake da su kudaden da ake kiyasin an sace a kasar "sun kai naira biliyan 595."

Ya ce ba don rashawa ba kudin da sun biya wa kasar bukata wajen ayyukan raya kasa da aka sanya cikin kasafin kudin bana don shirin ciyar da 'yan makaranta abinci da shirye-shiryen samar da ayyuka yi da kuma gina manyan tituna kamar guda bakwai.

Sai dai wadansu 'yan kasar suna sukar yaki da cin hancin da gwamnatin kasar take yi, inda suke zargin cewar an karkata ne a kan 'yan adawa.

Amma gwamnatin na musanta wannan zargin.