Allah ne ya dora ni kan makiya - Saraki

Bukola Saraki Hakkin mallakar hoto PHILIP OJISUA

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ya ce ba shi da abin godiya sai Allah wanda ya ce shi ne bashi nasara a shari'ar da aka shafe shekara uku ana yi masa.

Abubakar Bukola Saraki na mayar da martani ne kan wanke shi da Kotun Kolin kasar ta yi daga dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa na yin karya wajen bayyana kadarorinsa lokacin yana gwamnan Kwara.

Duka alkalan kotun kolin biyar sun amince da hukuncin, inda suka yi watsi da hukuncin kotun daukaka kara na cewa ya kamata Sanatan ya fuskanci tuhumce-tuhumce uku, suna masu cewa hujjojin da gwamnati ta gabatar raunana ne.

Wata sanarwa da Bukola Saraki ya sanya wa hannu da kansa, ta ce "hukuncin ya faranta min rai kuma ya karfafa min gwiwa kan kasar nan da kuma imani da Allah wanda Ya dora ni kan hukuncin bil'adama".

A shekarar 2015 ne gwamnatin Najeriya ta shigar da karan Saraki kan tuhume-tuhume 18 na yin karya wajen bayyana abin da ya mallaka.

Masu sharhi na ganin wannan ba karamar nasara ba ce ga Saraki, wanda batun shari'ar ya mamaye mulkinsa na majalisar ta dattawa a shekara ukun da ta gabata.

Sai dai duk da cewa sanata Saraki ya yi nasara a bangaren sharia mma kuma haryanzu akwaii tuhumar da hukumomin 'yan sanda suke yi masa.

'Yan sanda na bincike kan zargin da ake yi masa a kan cewa yana da hannu wajan tallafawa 'yan fashi da makamai.

Martanin Saraki

Bukola Saraki ya bayyana farin cikinsa kan hukuncin, wanda ya nanata matsayinsa na asali cewa siyasa ce kawai ta sa a ka shigar da karar tun farko.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An shafe kusan shekara uku ana yin wannan shari'a

"A karshen tafiya mai tsawon kwanaki 1018 da aka fara a ranar 22 ga watan Satumban 2015, ina farin ciki game da hukuncin da ya wanke ni" in ji Saraki.

"Hukuncin ya faranta min rai kuma ya karfafa min gwiwa kan kasar nan da kuma imani na ga Allah wanda Ya dora ni kan hukuncin bil'adama".

Shugaban majalisar dattijan ya ce tun farko yana da kwarin gwiwa a kan bangaren shari'ar kasar sai dai ya sake jaddada cewa akwai bita-da-kulin siyasa a tuhumar da ake yi masa .

"An shigar da wannan karar ne saboda na bayyana a matsayin shugaban majalisar dokoki kuma na yi hakan bata tare da amicewar wasu ba. Ina shakku a kan cewa akwai wani da zai so ya san ko na bayyana kadarori na a cikin shekara 15 da suka gabata.

Hakkin mallakar hoto NurPhoto
Image caption Wasu na ganin wannan shari'a na daga cikin abubuwan da suka sa dangantaka ta yi tsami tsakanin Bukola Saraki da Shugaba Buhari

Kamar sauran mutane, a bayyane take cewa yaki da rashawa da ake yi ana yinsa ne kan 'yan siyasa na bangaren hamayya".

A ranar Juma'a kotun Kolin Najeriya ta wanke Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki kan zargin karya wajen bayyana kadarorinsa.

Yadda shari'ar ta gudana

A watan Yunin bara ne Alkalin kotun da'ar ma'aikata Danladi Umar ya fara yin watsi da tuhume-tuhume 18 da ake wa Saraki.

Daga nan ne sai Ministan shari'ar kasar, Abubakar Malami, ya bayar da umarnin a daukaka kara a gaban kotun daukaka kara da ke Abuja.

Sai dai a hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke a watan Disambar bara, ya dawo da tuhume-tuhume uku cikin 18 da ake masa kuma ya umarce shi da ya koma kotun da'ar ma'aikata don ya sake kare kansa.

Daga nan ne sai Saraki ya daukaka kara zuwa kotun kolin, inda yake kalubalantar hukuncin kotun daukaka karar na dawo da tuhume-tuhume ukun.