Dan shekara uku ya mutu a shadda a Afirka ta Kudu

Yawancin shadda a na yinsu da karfe mai tsatsa. Hakkin mallakar hoto Corbis/Getty Images
Image caption Yawancin shadda ana yin su da karfe ne mai tsatsa a kasar

Wani yaro dan shekara uku ya rasa ransa bayan da ya fada cikin masai a kasar Afirka ta Kudu.

Omari Monono ya mutu ne a wani bandaki da ke wajen gidansu a lardin Limpopo, wurin da aka taba samun wani yaro mai sheharu biyar mai suna Micheal Komape ya mutu a shadda a shekarar 2014.

"Ina cikin matukar damuwa, ba na iya cin abinci, ba na iya bacci," a cewar mahaifiyar marigarin Kwena Monono.

"A kowane lokaci na ga wani abu da yarona yake so, sai zuciyata ta karaya sai kuma kuka ya zo mini."

An fito da yaron daga cikin shadda a ranar Laraba ne da misalin karfe hudu agogon can, sa'o'i biyu bayan bacewar yaron in ji mahaifiyarsa.

'Yan sanda sun ce innar yaron ta kai rahoton ne bayan ta neme shi ta rasa.

"Innarsa ta tube shi domin ya shiga ban daki kamar yadda ta saba sai ta koma cikin gida domin ta ci gaba da ayyukan gida, daga bisani sai ta lura yaron bai dawo ba, har lokaci mai tsawo" in ji wani mai magana da yawun 'yan sanda, Maphure Manamela.

Hakkin mallakar hoto Gallo
Image caption 'Yan uwa da abokan arziki a kabarin Micheal Komape, wani yaro da ya taba mutuwa a shadda a shekarar 2014

Masu fafutika sun fara kokarin gannin an biya iyalan marigayin diyyar Rand miliyan 3 (kimanin dala 221,000).

Wannan al'amarin ya jawo zanga-zanga, inda mutane ke cewa a rufe shadda domin kiyaye irin wannan abu daga sake faruwa.

Wannan ba shi ne karon farko da aka samu faruwar irin wannan al'amari ba, domin a farkon shekarar nan wata 'yar shekara biyar ta mutu a shadda a kudancin lardin Cape.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba