An daure tsohon firai ministan Pakistan shekara 10 a gidan yari

Nawaz Sharif. Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Images
Image caption Nawaz Sharif ya musanta zargin da ake masa

Wata kotu a Pakistan ta yanke wa tsohon firai ministan kasar Nawaz Sharif hukuncin daurin shekara 10 a gidan yari bayan samunsa da laifi a tuhumar rashawa da ake yi masa na mallakar gidajen kasaita hudu a birnin Landan.

Wata kotun tabbatar da gaskiya da adalci ce ta yanke hukuncin bayan jinkirin da aka rika fuskanta daga bisani.

An yanke masa hukuncin ne tare da diyarsa, Maryam Nawaz Sharif, wadda ita kuma yanke wa hukuncin daurin shekara bakwai, yayin da aka yanke wa surukinsa, Safdar Awan, hukuncin daurin shekara guda.

Nawaz Sharif ya ce akwai bita-da-kulin siyasa a hukuncin.

Sai dai dukkansu ba sa kasar lokacin yanke hukuncin.

A halin yanzu Mista Sharif da diyarsa suna Landan, inda matarsa Kulsoom Nawaz ta ke jinyar cutar sankara.

Mai shari'a Mohammad Bashir ya umarci Sharif ya yi shekara 10 a gidan yari saboda ya mallaki kadarorin da suka fi karfin albashin da ake biyansa, sai kuma shekara guda a gida yari saboda ya ki ba da hadin kai a binciken da kotun ta gudanar.

Kodayake za a yi masa dukkan hukuncin ne a lokaci guda.

Hakazalika Sharif zai biya diyyar dala miliyan 10.6 yayin da Maryam za ta biya dala miliyan biyu.

Shari'ar wadda aka yi wa lakabi da Avenfield Reference, ta shafi wasu kadarori da ke babban birnin kasar Birtaniya.

Sai dai takardun Panama da aka kwarmata a shekarar 2015 sun bayyana cewa dangin Shariff nada alaka da wasu kamfanonin ketare.

Amma iyalinsa sun jaddada cewa ta halaltacciyar hanya suka mallaki gidajen.

Labarai masu alaka