Gyara Ajaokuta ya fi dace wa da kudaden Abacha - Majalisa

Gyara Ajaokuta ya fi dace wa da kudaden Abacha - Majalisa

Majalisar wakilan Najeriya ta ce ta fi so a yi amfani da kudin da Abacha ya boye a Switzerland wajen farfado da kamfanin Ajaokuta, maimakon raba wa talakawa.

Majalisar ta wakilai ta ce sanya kudin a wasu ayyuka kamar karasa aikin masana'antar sarrafa karafa ta Ajaokuta da za ta samar da ayyuka ga dubban matasa.

To sai dai wasu matasan kasar suna da ra'ayin da ya saba da na majalisar.