Dino Melaye ya fitar da bidiyo yana rawar 'ficewa daga APC'

Dino Melaye Instagram

Asalin hoton, Dino Melaye

Sanatan jam'iyyar APC Dino Melaye ya fitar da hoton bidiyo yana rawa tare da yi wa jam'iyyar adawa ta PDP waka.

Melaye ya wallafa bidiyon ne a shafukansa na sada zumunta na Facebook da Twitter da Instagram.

'PDP! Oh gidana, gidana, gidana, yaushe ne zan ga gidana? APC ta wahalar da ni sosai, ba zan taba mantawa da gidana ba."

Tuni bidiyon ya ja hankalin jama'a sosai a shafukan sada zumunta na intanet, musamman yadda ya fito yana rawa da kuma wakar da ya rera ta PDP.

Wasu na ganin a matsayinsa na Sanata da ke wakiltar jama'a bidiyon bai dace ba, yayin da wasu kuma ke ganin yanzu rawa wani sabon salon nuna annashawa da nasara ne a fagen siyasar Najeriya.

Wata a shafin facebook ta ce ba ta cika kula da sha'anin Sanata Dino Melaye ba amma ganin bidiyon nan na ban dariya, ya zama dole ta yada ga mabiyanta.

El Sadeeq Abubakar kuma ya yada bidiyon na Sanata Melaye a Facebook tare da tambayar 'ko wannan ya cancanci ya zama shugaba?

Wasu na ganin bidiyon sanatan ya tabbatar da ya yi watsi da APC ya koma jam'iyyar da ya fito PDP.

Sanata Melaye wanda aka zaba a matsayin dan majalisar wakilai karkashin jam'iyyar PDP a 2007, ya canza sheka zuwa APC inda aka zabe shi matsayin sanata a jihar Kogi a zaben 2015.

Sai dai kuma Sanatan wanda yake da kusanci da shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki ya dawo yana adawa da gwamnatin shugaba Buhari ta APC.

Kuma ya fitar da wannan bidiyon ne bayan kotun koli ta wanke mai gidansa Sanata Bukola Saraki daga zargin yin karya wajen bayyana kadarorin da ya mallaka lokacin yana gwamnan Kwara.