An fitar da Rasha daga gasar cin kofin duniya

Croatia ta fitar da Rasha daga gasar cin kofin duniya

Asalin hoton, Getty Images

Tawagar kwallon kafa ta Ingila ta kai wasan daf da karshe a gasar cin kofin duniya da ake yi a Rasha.

Ingila ta kai wannan matakin ne bayan da ta doke Sweden da ci 2-0 a karawar da suka yi a ranar Asabar.

Tawagr kwallon kafa ta ci kwallon farko ta hannun Harry Maquire sannan Dele Ali ya ci na biyu, kuma hakan ya kai Ingila was an daf da karshe a gasar cin kofin duniya a karon farko tun bayan wadda aka yi a Italiya a 1990.

Wannan ne kuma karo na hudu da Ingila ta kai was an daf da karshe a gasar cin kofin duniya, idan ka hada da kofin duniya daya tal da ta lashe a 1966 a lokacin da ta karbi bakuncin gasar.

Ita kuwa Mai masaukin baki Rashi ta yi rashin nasara ne a hannun Croatia bayan da suka tashi 2-2 a minti 120 da suka kece raini a tsakaninsu.

Rashan, ta yi ban kwana da gasar cin kofin duniyar ne bayan da Croatia ta fitar da ita a bugun fenariti.

Croatia ta yi nasara cin fenariti 4-3, za kuma ta yi gumurzu da Ingila a wasan daf da karshe a ranar Laraba 11 ga watan Yuli.

Karanta wasu karin labaran