An ceto wasu yaran da suka makale a kogo a Thailand

Tun a ranar 23 ga wayan Yuni yaran 'yan shekara tsakanin 11 zuwa 17 sun makale a kogon tare da mai horar da su Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tun a ranar 23 ga wayan Yuni yaran 'yan shekara tsakanin 11 zuwa 17 sun makale a kogon tare da mai horar da su

An yi nasarar fito da wasu daga cikin yaran da suka makale a wani kogo a arewacin Thailand makwanni biyu da suka gabata.

Jami'ai a kasar Thailand sun ce an fito da kusan rabin yawan yaran wato guda shida a ranar Lahadi.

Masu aikin ceto sun yanke shawarar gudanar da aikin ceton mai hatsarin gaske saboda gudun kada ruwa ya kara cika kogon.

Yaran su shafe watanni suna jiran ruwa ya yi kasa domin a fitar da su.

Ma su ninkaya ne suke jagorantar ceto yaran da kuma mai horar da su a cikin yanayi mai hatsarin gaske har zuwa bakin kogon Thanm Luang da suka makale.

Ba za a iya fitar da yaran ba lokaci guda, kuma babu tabbacin tsawon lokacin da za a dauka kafin kammala aikin ceton.

Sai dai aikin na tafiya da sauri fiye da yadda hukumomi suka yi hasashe tun da farko.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jirgin da zai kwashe yaran ya isa wurin

Wakilin BBC da ke wurin ya ce Narongsak Osottanakorn da jagorantar aikin, ya ce: "yau ce ranar, kuma yaran sun nuna sun shirya wa kalubalen da ke gabansu.

Ya kara da cewa likitoci da suka diba yaran sun ce yaran na cikin koshin lafiya kuma sun shirya.

Ana fito da yaran ne ta hanyar amfani da kayan ninkaya da suka hada da abun shakar iska da gilashin ruwa, kuma duk yaro daya kwararru biyu ne ke kula da shi a yayin kokarin fito da su daga kogon.

Yaran wadanda dukkaninsu maza ne tare da kocinsu na kwallon kafa, kusan mako 2 ke nan da suka makale a kogo sakamakon wata ambaliyar ruwa da aka yi.

Hakkin mallakar hoto FACEBOOK/EKATOL

Wadansu masu aikin ceto 'yan kasar Birtaniya ne suka gano yaran bayan kwashe fiye da mako guda ana nemansu a Chiang Rai da ke arewacin Thailand.

Yaran sun je kogon ne a ranar 23 ga watan Yuni don yawon bude ido.

Tun sanar da gano inda suka makale, ma'aikata fiye da 1000 suka tafi aikin ceto wadanda suka fito daga kasashen China da Myanmar da Laos da, Australia da Amurka da kuma Birtaniya.

Hakkin mallakar hoto GAVIN NEWMAN
Image caption Wadannan 'yan Birtaniyar ne suka ganao yaran