PDP ta yi kawance da jam'iyyu 40 'don kayar da Buhari'

Atiku Hakkin mallakar hoto Twitter/PDP

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP ta kulla wani sabon kawance da wadansu jam'iyyu fiye da 40 da ke kasar, gabanin babban zaben shekarar 2019.

Jam'iyyun sun sanar da hakan ne lokacin wani taro da suka yi a Abuja ranar Litinin, inda suka yi wa kawance lakabi da Coalition of United Political Parties (CUPP).

Sanarwar ta biyo bayan sanya hannu kan wata yarjejeniya da suka cimma da shugabannin jam'iyyun,"don kayar da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019," a cewarsu.

Yarjejeniyar ta kunshi wani shiri ta yadda za su tsayar da dan takara daya tilo a zaben shugaban kasa, da na gwamnoni a jihohi da kuma kujerun majalisa.

Sai dai zuwa yanzu jam'iyya mai mulki ta APC ba ta mayar da martani ba, game da batun.

Hakkin mallakar hoto Twitter/@Atiku
Image caption Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar bayan taron

Cikin wadanda suka halarci taron har da shugaban sabuwar jam'iyyar APC Injiniya Buba Galadima da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar da kuma mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu da sauransu.

A shekarar 2015 ne jam'iyyar APC ta doke PDP a babban zaben kasar, bayan ta shafe shekara 16 tana mulkin kasar.

Waiwaye

A makon da ya gabata ne tsoffin 'yan sabuwar PDP da suka hada da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da kuma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suka kirkiro wani bangare a cikin jam'iyya mai mulkin Najeriya APC, da sunan Reformed APC, ko rAPC.

An dade ana takun-saka tsakanin wadanda suka shigo jam'iyyar kafin zaben 2015 da ake kira 'yan sabuwar PDP da kuma bangaren gwamnatin APC.

'Yan sabuwar PDP sun yi zargin cewa ba a damawa da su a gwamnatin APC tare da barazanar daukar mataki idan har ba a biya bukatunsu ba.

Sannan a wani bangaren kuma ana tafiya ne da sunan jam'iyya daya amma akwai masu hamayya da juna a APC musamman a jihohi da dama da jam'iyyar ke mulki.

Tasirin kawance a 2015

Wannan abu dai na daya daga cikin manyan al'amuran siyasa da ya faru a Najeriya zuwa yanzu, a yayin da kasar ke shirye-shiryen gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki a watan fabrairun 2019.

Irin wannan al'amari ne ya faru a shekarar 2015 wanda ake ganin shi ne ya janyo shan kayen da jam'iyyar APC ta yi wa tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.

Amma a halin yanzu babu tabbas kan ko wannan gamayyar kawance za ta samu damar cimma manufarta a zabe mai zuwa.

Sai dai masu sharhin siyasa na ganin rigingimun APC da ta ke fama da su na iya yi wa jam'iyyar illa sosai a zaben 2019.