Cogen NYSC: Me ya sa gwamnatin Buhari ta yi gum kan Kemi Adeosun

Kemi Adeosun da Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ne ya nada Mrs Adeosun ministar kudi a 2015, kuma shi ya rantsar da ita

Gwamnatin Najeriya ta ki cewa komai game da zargin da aka yi wa ministar kudin kasar na yin amfani da takardar shaidar hidimar kasa ta "jabu".

Jaridar Premium Times ta ce ta bankado yadda Kemi Adeosun ta ki halartar aikin hidimar kasa bayan kammala karatunta a Birtaniya 1989, amma daga bisani ta mallaki takardar "jabu" da ke nuna cewa an dauke mata yin hidimar.

Lamarin na ci gaba da jan hankalin masu lura da al'amura da ma sauran 'yan kasar, musamman a shafukan sada zumunta.

BBC ta yi yunkurin jin ta bakin ministar amma mai magana da yawunta Oluyinka Akintunde bai dauki wayarmu ba, kuma bai bayar da amsar sakon da aika masa a rubuce ba.

Mai magana da yawun Shugaba Muhamnmadu Buhari Malam Garba Shehu, ya shaida wa wakilinmu cewa kamata ya yi "a ji ta bakin ministar tukunna kafin a zo kanmu".

Wannan shi ne bayanin da abokin aikinsa Femi Adesina ya yi mana lokacin da muka tuntube shi.

Ba mu samu jin ta bakin NYSC ba, amma Premium Times ta ce a ranar Litinin sun shaida wa wakilinsu cewa suna ci gaba da bincike kan bukatar da suka gabatar musu, kuma za su bayar da amsa da zarar sun kammala bincike.

Yadda labarin ya fito

Dan jaridar Premium Times Abdul'aziz Abdul'aziz ne ya bankado labarin, inda ya bi kwakwaf domin gano inganci ko sahihancin takardun da ministar ta gabatar da ke nuna cewa an dauke mata halartar aikin hidimar kasar.

Bayan binciken ne kuma, wanda ya dauki lokaci ana gudanarwa, jaridar ta ce ta gano cewa shaidar da Misis Adeosun ta gabatar ta boge ce.

Bayan kammala karatunta a shekarar 1989, tana da shekara 22 da haihuwa a Polytechnic of East London.

Ya kamata a ce Misis Adeosun ta zo Najeriya domin yin aikin hidimar kasa, amma sai ta ki yin hakan, inda ta fara aiki a Birtaniya.

Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Kemi Adeosun na fuskantar matsin lamba daga sassa daban-daban

Ta yi ayyuka da dama da suka shafi fannin tsumi da tattalin arziki wanda shi ta karanta a jami'a.

Ta koma Najeriya a shekarar 2002, amma duk da haka ba ta je ta halacci NYSC ba, sai kawai ta ci gaba da aiki a wani kamfani mai zaman kansa mai suna, Chapel Hill Denham, kamar yadda Premium Times ta bayyana.

Kwatsam a shekarar 2009 sai ta yanke shawarar karbar takardar shaidar boge wacce ta nuna cewa an amince ka da ta halacci aikin hidimar kasar, a cewar Premium Times.

Tsarin hukumar NYSC ya nuna cewa ba a bai wa duk mutumin da ya kammala makaranta yana/tana kasa da shekara 30 (kamar Misis Adeosun) damar kin halattar hidimar kasa.

Wasu jami'ai a hukumar da ba su amince a bayyana sunansu ba, sun shaida wa jaridar cewa shaidar da ta bayar ta boge ce, domin daraktan da ya sanya wa takardar hannu ya mutu watanni takwas kafin a bayar da takardar ta ta.

Tarihin karatun Kemi Adeosun

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ne ya nada Mrs Adeosun ministar kudi a 2015, kuma shi ya rantsar da ita
  • An haife ta a shekarar 1967
  • Ta yi digiri a makarantar Polytechnic of East London
  • Makarantar ta sauya suna zuwa University of East London a 1992
  • Ta yi aiki a kamfanoni da dama a Birtaniya
  • Ta dawo Najeriya a 2002, inda ta fara aiki da Chapel Hill Denham

Manyan ayyukan da ta yi

Duk da cewa tana amfani da takardar shaidar "jabu" Misis Adeosun ta ci gaba da aiki a Najeriya, inda ta rike manyan mukamai.

  • Quo Vadis Partnerships - manajan darakta
  • Kwamishinar kudi ta jihar Ogun
  • Ministar kudi ta gwamnatin Najeriya

Labarai masu alaka