George Clooney ya yi hadari a babur

George Clooney Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Al'amarin ya rutsa da jarumin ne yayin da yake shirya wani sabon fim

An garzaya da jarumin fina-finan Hollywood George Clooney zuwa asibiti bayan ya samu rauni sakamakon taho-mu-gama tsakanin babur dinsa da wata mota.

Lamarin ya faru ne a tsibirin Sardinia, inda jarumin dan Amurka ke shirya wani fim na Channel 4 Catch-22.

Wata jami'a a yankin ta tabbatar wa da BBC cewa Clooney ya samu rauni, amma ba mai muni ba.

Ta kara da cewa a yanzu an sallame shi daga asibiti.

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Jarumin a wurin wani taron fina-finai da aka yi bara

Clooney yana yawan zuwa Italiya kuma anan ne ya auri matarsa Amal a 2014.

Amal, wacce lauya ce mai fafutukar kare hakkin dan'adam, ta haifi 'yan biyu, Ella da Alexander, a 2017.

Clooney ya taba lashe lambar yabo ta Oscar a matsayin jarumi, ya yi fice a fina-finan da ya taka kamar Ocean's 11, da Up in the Air, da Michael Clayton da O Brother, Where Art Thou?

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Jarumin tare da mai dakinsa lokacin da suka halarci bikin gidan sarautar Birtaniya

Labarai masu alaka