Shan barasa ya tsayar da zirga-zirgar jiragen kasa a India

Al'ummar kasar Indiya da dama ne ke amfani da jirgin kasa a kowacce rana Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mahukunta sun ce an samu tsaikon zirga-zirgar jiragen kasa da dama a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin kasar Indiya, bayan da aka samu mai kula da zirga-zirgar jiragen na bacci bayan ya yi mankas da barasa.

Deep Singh, ya kasa daukar kiran wayoyin da aka rinka yi masa domin ya bayar da umarnin wucewa ko kuma tashin jiragen saboda bacci mai nauyin da ya dauke shi.

Rashin amsa kiran wayar ya sa wasu jami'ai suka yi maza suka je inda ya ke a tashar jirgin kasa ta Murshadpur domin ganin ko lafiya.

Kafar yada labarai ta kasar ta ce, jami'an sun tarar da Mr Singh a cikin ofishinsa ya na ta sharar bacci, ga kuma kwalbar giya da aka shanye a gefensa.

Tuni dai aka bayar da umarnin gudanar da bincike a kan Mr Singh, inda wasu rahotanni suka ce sakamakon binciken farko da aka yi masa a asibiti, an gano cewa akwai giya mai yawa a cikin jininsa.

Wani babban jami'i a bangaren sufurin jiragen kasa a jihar ya ce, "Mr Singh ya sha giya ne sosai da har ta kai ko tafiya ma ba zai iya yi ba, kuma wannan matsala ce babba a bangaren lafiyarsa da kuma wajen aikinsa."

Wasu majiyoyi sun ce jiragen kasa da dama da suka isa tashar jirgin da Mr Singh ke aiki sun tsaya saboda ba a basu alamar cewa su wuce ba.

Kuma jirage da dama ne ke wucewa ta tashar a ko wacce rana.

Ba kasafai ake samun irin wannan matsala ba dai a Indiya.

Karanta wasu karin labaran