World Cup 2018: Faransa, Belgium, da Ingila 'na rawa da bazar 'yan ci-rani'

The French team line up before a match with Uruguay Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tawagar Faransa da ta fara wasan dab da na kusa da na karshe da Uruguay tana da 'yan wasa biyar wadanda iyayensu 'yan ci-rani ne: (A baya, hagu zuwa dama): Paul Pogba da Samuel Umtiti; (sahun gaba) Corentin Tolisso da N'Golo Kante da kuma Kylian Mbappe

Uku daga cikin tawagogi hudu da suka rage a gasar cin kofin duniya suna kamanceceniya sosai, ba ta wajen kusancin kasashensu ba kawai.

Akwai bakaken fata 'ya'yan 'yan ci-ranin Afirka da dama a tawagogin Faransa da Belgium da Ingila. Bari mu duba yawansu:

Idan aka duba salsala za a ga cewa a kalla iyayen mutum 16 daga cikin 23 na tawagar kasar Faransa ba a kasar aka haife su ba.

Sannan akwai wasu biyun kuma da su ma aka haife su a tsibiran yankin Karibiyen, wadanda ake daukarsu wani bangare na Faransa.

'Yan wasan Belgium 11 da na Ingila shida 'ya'yan 'yan ci-rani ne na kusa, yayin da wasu 'yan wasan Ingila hudu kuma suka kasance tsatsonsu na ainihi daga Afirka ne.

Daya daga cikinsu Raheem Sterling an haife shi ne a Jamaica.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mahaifin Mbappe, Wilfred, ya yi kaura ne daga Kamaru zuwa Faransa

Tawagar Faransa mai kunshe da mutane daban-daban ba abar mamaki ba ce.

An yi ta murnar nasarar da tawagar ta yi a gasar cin kofin duniya ta 1998, wanda daga wannan lokacin ba ta kara nasara ba, a matsayin nasarar bangarori daban-daban, har aka yi wa tawagar lakabi da "Tawagar Bakan Gizo."

Sai dai kuma, bayan shekara hudu, 'yan wasa masu ruwa biyu sun yi barazanar kaurace wa tawagar a wani mataki na nuna rashin kin amincewa da nasarar da dan takara Jean-Marie Le Pen mai ra'ayin rikau ya samu a zagayen farko na zaben shugaban kasar na shekarar 2002 (duk da cewa ya sha kaye a zagaye na biyu na zaben).

A zaben bara, masu ra'ayin rikau sun sake yin hakan inda 'yar Mr Le Pen, Marine, ta samu kashi 33 cikin 100 na kuri'u, abin da ya rubanya kuri'un da jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta National Front ta samu a zaben 2002.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 16 daga cikin 'yan wasa 23 na Faransa 'ya'yan 'yan ci-rani ne

“Marine Le Pen ta nuna takaicinta na cewa idan ta kalli Les Bleus (lakabin tawagar 'yan kwallon Faransa), ’ba ta gane Faransa ko ita kanta,’" kamar yadda Afshin Molavi, daga banagaren nazari mai zurfi kan harkokin kasa-da-kasa na jami'ar Johns Hopkins da ke Washington ya bayyana.

Babu barazanar kauracewa a wannan lokacin , sai dai kuma, gabannin wasannin dab da na karshe, Faransa za ta kasance kasar da kowa ke ganin za ta dauki kofin.

Tawagar Belgium tana da 'yan wasa 11 da ke da akalla daya daga cikin iyaye 'yan ci-rani ciki har da Romelu Lukaku da Vincent Company, wadanda iyayensu 'yan Congo ne - mahaifin Lukaku ya taka wa tawagar kasar Zaire leda a shekarun 1990.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A cikin 'yan wasan Belgium da ta fara wasanta da Brazil da su, daya daga cikin yan wasa biyar iyayensa 'yan ci-rani: (Sahun baya, hagu zuwa dama) Romelu Lukaku (DR Congo); Axel Witsel (Martinique); Vincent Company (DR Congo); Marouane Fellaini (Morocco); Sahun gaba: Nacer Chadli (Morocco)

Wannan ya bambanta da tawagar kasar a gasar kofin duniya ta 2002, a lokacin da 'yan wasa biyu ne kawai suka kasance ba 'yan asalin kasar Belgium ba.

Gasar da ake yi Rasha na zuwa ne a wani lokacin da ake samun rarrabuwar kai a fagen siyasa da al'ada da zamantakewa a Belgium, wata kasa mai manyan yankuna biyu da harsuna biyu - Wallonia (harshen Faransanci) da Flanders ( harshen Flemish).

Zaman doya da manja da ake yi tsakanin bangarorin biyu ya haddasa yunkurin balewa daga kasar a lokuta daban daban kuma a zaben shekarar 2010, nasarar jam'iyyar masu kishin kasa na harshen Flemish na N-VA ya janyo rikicin siyasa, wanda ya sa kasar ta kasa kafa gwamnati cikin kwanaki 541.

Ta haka, tawagar mai 'yan wasa daga yakunan biyu da kuma kocinsu na wakiltar hadin kai, kuma domin 'yan tawagar suna wasansu ne a Ingila, harshen Shakespeare ya zama hanyar magana gare su..

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Murnar Belgium da tawagar ya dara bambance-bambancen kabilanci da na al'ada

“Ni ba na gasar kofin domin in tattauna siyasa. Wannan gasar wayta dama ce ta murna a matsayin mu na 'yan kasa da kuma mara wa wata tawaga da ke wakiltar daukacin al-ummar Belgium,” In ji wani masoyin tawagar Belgium, Jan Aertssen, wadda ta tattauna da BBC gabanni nasarar tawagar kan Brazil a Kazan.

“Mutanen da ke kare warewa ba su yi tunanin irin raunin da tawagar ka iya samu ba,” in ji shi.

'Ya'yan 'yan ci-rani sun samu wakilci mai kyau a tawagar Ingila.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tawagar Ingila da kara da Sweden a wasan kusa da dab da na karshe tana da 'ya'yan 'yan ci-rani hudu: (sahun baya, hagu zuwa dama) Ashley Young (Jamaica); Dele Alli (Nigeria); (Sahun gaba) Harry Kane (Ireland); Raheem Sterling (Jamaica)

Nasarar bazata da koci Gareth Southgate ya samu -wadda ta kunshi 'yan wasa shida wadanda akalla daya daga cikin iyayensu suka kasance 'yan ci-rani a Birtaniya, da Raheem Sterling wanda aka haifa a Jamaica - yana jan hankalin masu goyon bayan tawagar.

“Mu 'yan tawaga ce da ta kunshi mutane masu asali daban daban, masu kuruciya da ke wakiltar Ingila. A Ingila mun shafe wani lokaci muna tunanin mene ne ainihinmu na yanzu. Da gaske, da farko za a yanke mini hukunci ne game da sakamakon wasan kwallon kafa . Muna da damar yin tasiri kan wasu abubuwan da suka fi haka girma," in ji Southgate.

Amma kwararru kan mu'amala tsakanin kabilu sun bayar da shawarar cewa mutane su yi hankali. Piara Powar, wanda shi ya samar da FARE Network, wata kungiya da ke nazari kan matsalolin wariyar launin fata a kwallon kafar Turai , ya yi gargadin cewar tawaga mai mutane daban-daban ba ta yawan samun tasiri mai dadewa akan mutane.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An haifi Raheem Sterling (a hagu) ne a Kingston, Jamaica