Ambaliya 'ta hallaka' mutum 155 sakamakon ruwan sama a Japan

Soldiers carry an elderly woman to a vehicle to be evacuated after rescuing her following heavy flooding Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan ya kasance mafi yawan mutuwa da ruwa sama ta haifar a kasar tun 1982, inda kimanin mutane 300 suka mutu.

A kalla mutum 141 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da zaftarewar laka sanadiyyar ruwan sama mai tsanani a yammacin Japan, in ji gwamnatin kasar.

It is the highest death toll caused by rainfall that Japan has seen in more than three decades.

Wannan al'amari ya jawo mutuwar yawan mutanen da ba a taba samu ba sakamakon ruwan sama cikin shekara 30 a Japan.

Masu aikin ceto suna tona cikin laka da baraguzai don neman wadanda ba su mutu ba, yayin da ake cigaba da neman mutane da yawa.

An kwashe mutane kusan miliyan biyu daga yankin, bayan da koguna suka cika suka batse.

Hukumomi sun bude makarantu da wuraren motsa jiki domin su zama mafaka ga wadanda ruwan saman ya raba da muhallansu.

Har yanzu ana fuskantar barazanar zaftarewar laka da tsaunuka da suke nuna alamar ruftawa.

"Na gaya wa iyalina su yi shirin ko-ta-kwana," a cewar Kosuke Kiyohara, mai shekara 38, wanda bai ji duriyar 'yar uwarsa da 'ya'yanta biyu ba, kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Firai Ministan kasar, Shinzo Abe, ya soke wata ziyarar kasashen waje don magance iftila'in ambaliyar.

Fiye da ma'aikatan ceto 70,000, ciki har da ma'aikatan kashe gobara da sojoji ne, ke taimakawa wajen aikin ceto.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An tura ma'aikatan gaggawa fiye da 70,000 a fadin yammacin Japan
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kimanin mutum 12,000 suna zama a sansanonin wucin gadi a yankuna 15
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Motoci da gidaje sun lalace sanadiyyar ruwa mai tsanani, yayin da wurare suka cika da tarkace da laka
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ambaliya ta cimma dubban gidaje ta kuma yi sanadin daukewar wutar lantarki da ruwan famfo
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tun ranar Alhamis da ta gabata aka yi ta sheka ruwa a wasu sassa na yammacin Japan fiye da yadda aka saba a watan Yuli
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jami'ai sun yi gargadi game da ruwan sama da hadari da zaftakewar laka

Har ila yau, an yi gargadin yiwuwar samun ambaliyar ruwa a wasu yankunan da suka hada da yankin Okayama a kudancin kasar Japan.

Amma ana tsammanin yanayin zai daidaita nan da kwanaki kadan masu zuwa wanda zai iya taimakawa wajen ayyukan ceto.

Wani jami'in gwamnatin tarayya yashaida wa AFP cewa: "Muna duba gida-gida don ganin ko akwai mutanen da suka makale a ciki. Mun san cewa lokaci zai iya kure mana, amma muna kokarin sosai iyakar iyawarmu."

Labarai masu alaka

Karin bayani