Shugaban Turkiyya ya nada surukinsa Ministan Kudi

Jawabin shugaba Recep Tayyip Erdogan bayan da aka rantsar da shi 9 Juli 2018 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mista Erdogan ya fada wa bakin da suka je fadar shugaban kasa cewa "Turkiyya ta bude sabon babi"

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya nada surukinsa a matsayin ministan kudi bayan da ya sha rantsuwar kama aiki na wa'adin shekara biyar.

Nadin Berat Albayrak ya janyo rashin tabbas a kasuwar hannayen jari game da damuwar da aka nuna a kan yadda shugaban kasa ke fifita danginsa kan wasu a harkokin gwamnati.

Mr Erdogan, wanda aka sake zaba a watan da ya gabata, ya sha alwashin "kawo ci gaba a kasar" ta hanyar amfani da sabon ikon da aka ba shi.

Sai dai 'yan adawa na fargabar shugaban kasar zai yi wa mulkin dimukradiya karan-tsaye.

Sabon mukamin Mr Erdogan zai sa majalisar dokoki da kuma ofishin Firai Minista su daina tasiri, wanda shi ne tsarin da ake amfani da shi tun bayan kafuwar kasar a matsayin jamhuriya ta zamani, shekaru 95 da suka gabata.

Mukamin zai ba shi damar nada ministoci da mataimakin shugaban kasa tare da yin katsalandan a cikin harkokin shari'a.

Bayan da ya sha rantsuwa a Majalisar dokoki a ranar Litinin, Erdogan ya fada wa bakin da suka je fadar shugaban kasa da ke Ankara babban birnin kasar cewa, Turkiyya "ta bude sabon babi."

"Za mu daina amfani da tsohon tsarin da a baya ya jefa kasarmu a cikin rikicin siyasa kuma ya janyo koma bayan tattalin arziki," in ji shi.


Erdogan - 'Mai janyo rarrabuwar kawuna'

Sharhin wakilin BBC a Turkiyya, Mark Lowen

Turkiyya ta shafe shekara 95 tana amfani da tsarin da ke bai wa majalisar dokoki iko, sai dai tun daga ranar Litinin ce tsarin ya zo karshe, bayan da sabon tsarin da shugaban kasa yake da iko ya fara aiki karkashin Recep Tayyip Erdogan.

Sakamakon galabar da ya samu, yanzu ya zama shugaban kasa mai cikakken iko, wanda yake da iko kan sojoji da jami'an leken asiri, kuma zai zartar da doka tare da zabar manyan alkalai.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bakin da suka halarci bikin rantsar da Shugaba Erdogan sun rinka kare kansu daga ruwan sama a lokacin bikin

Ga magoya bayansa, wannan wani tsarin siyasa ne mai karfi. Sai dai a wurin 'yan hamayya, mutum daya tilo yake mulki kuma zai kawo nakasu a mulkin dimukradiyar kasar.

A yanzu Mista Erdogan shi ne shugaban kasa mai karfin fada a ji tun bayan Ataturk: wanda shi ne ya kafa Turkiyya a gwamnati mai sassaucin ra'ayi, wanda ya dauki Turkiyya a matsayin kasar da ke yamma.

Sai dai Shugaba Erdogan ya sa adini a gaba wajen tafiyar da harkokin kasar kuma ya nesanta kansa daga kasashen yamma.

Shugabannin Turai kalilan ne suka halarci bikin rantsar da shi - kasashen Hungary da Bulgaria ne kawai suka je, sai shugabannin Afirka da kasashen Larabawa - alama da ke nuna yadda ya karfafa dangantarsa da wasu kasashen duniya.

Mista Erdogan na ta janyo ra'ayoyi mabanbanta kuma akwai rarrabuwar kawuna tsakanin al'umar kasar a yanzu.

Ga wasu dai, suna ganin an bude wani sabon babi ne a Turkiyya, wasu kuwa na ganin an wargaza jamhuriyar da marigayi Artaturk ya kafa ne.


Bayan labarin da aka samu kan nadin da Mista Erdogan ya yi wa surukinsa, darajar kudin kasar wato Lira ta fadi da kashi uku.

Berat Albayrak, mai shekara 40 shi ne mijin babbar diyar shugaban kasar, kuma shi ne ministan makamashi tun daga shekarar 2015, sai dai mukamin baya-bayan nan da ya samu ya sa wasu sun nuna fargaba kan adda ake fifita wasu a cikin gwamnati.

Ta bayyana cewa Mehmet Simsek, wanda tsohon ma'aikacin banki ne a Merrill Lynch, wanda kuma yake rike da mukamin maitaimakin Firay Minista a tsohuwar gwamnati, ba zai samu wani mukami ba a cikin wannan gwamnati.

A wani sauyi mai muhimmanci da Mista Erdogan ya yi shelarsa a ranar Litinin shi ne Manjo Janarar Hulusi Akar, da aka bayyana a matsayin sabon hafsan tsaron kasar.

Sai dai Mevlut Cavusoglu har yanzu yana rike da mukaminsa na ministan harkokin waje.

A watan da ya gabata ne aka sake zabar Mista Erdogan, inda ya lashe kashi 53 na kuri'u. Ya jagoranci kasar mai karfin tattalin arziki kuma ya kara samun magoya baya.

Sai dai ya sa an samu ra'ayoyi mabambanta a kasar, kuma ya sa a kama 'yan adawa inda ya sa wasu mutane 160,000 a gidan kaso.

Labarai masu alaka