An ceto dukkan yaran da suka makale a kogo a Thailand

A video grab handout made available by the Thai Navy Seals shows some members of the trapped football team, 4 July 2018 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yaran 'yan tsakanin shekaru 11 zuwa 17 sun makale ne yayin da suka je ziyarar bude ido

Masu nutso a ruwa a Thailand sunceto dukkan mutane 13 sa suka makale a kogo bayan da ruwa ya yi ambaliya cikin kogon, inda suka shafe kwana 17 kafin a kamala fito da su.

Halin da yaran 12 duk maza suka samu kansu a ciki da kuma mai horar da su kwallo, da aikin da aka yi ta yi na kokarin ceto su ya jawo hankalin al'ummar duniya sosai.

Sojojin ruwan Thailand sun ce a ranar Talata da yamma (agogon kasar) ne aka kammala aikin ceton ta hanyar fiddo da sauran yara hudu da kocinsu.

Tawagar yaran wadanda 'yan wata kungiyar kwallon kafa ce, sun makale ne a cikin kogon ranar 23 ga watan Yuni bayan da ruwan saman da aka sheka kamar da bakin kwarya ya jawo ambaliya.

Yaran 'yan tsakanin shekaru 11 zuwa 17 sun makale ne yayin da suka je ziyarar bude ido.

Labarai masu alaka

Karin bayani