Babu ruwanmu da su Buba Galadima – APC

Buhari Hakkin mallakar hoto Facebook/Nigeria Presidency
Image caption A watan jiya ne jam'iyyar APC ta yi babban taronta a Abuja, wanda ya bar baya da kura

Jam'iyyar APC ta mayar da martani game da kawancen da bangaren Buba Galadima wato rAPC ya kulla da gamayyar wadansu jam'iyyu 40 ciki har da PDP don kayar da Shugaba Muhammadu Buhari a babban zaben shekarar 2019.

Wata sanarwar da Sakataren Yada Labarai na Jam'iyyar Mallam Bolaji Abdullahi ya fitar ta ce: "babu wani bangare a jam'iyyar APC."

Ya ce jam'iyyarsu tana nan har yanzu a matsayin tsintsiya madaurinta daya a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.

Sai dai kuma ya ce a shirye suke su tattauna kan duk wata rashin jituwa da ta kunno kai "tsakanin mambobinta na hakika."

A ranar Litinin ne babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP ta kulla wani sabon kawance da wadansu jam'iyyu fiye da 40 da ke kasar, da nufin doke jam'iyyar APC a babban zaben shekarar 2019.

Jam'iyyun sun sanar da hakan ne lokacin wani taro da suka yi a Abuja, inda suka yi wa kawancen lakabi da Coalition of United Political Parties (CUPP).

Waiwaye

A makon da ya gabata ne tsoffin 'yan sabuwar PDP da suka hada da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da kuma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suka kirkiro wani bangare a cikin jam'iyya mai mulkin Najeriya APC, da sunan Reformed APC, ko rAPC.

An dade ana takun-saka tsakanin wadanda suka shigo jam'iyyar kafin zaben 2015 da ake kira 'yan sabuwar PDP da kuma bangaren gwamnatin APC.

Hakkin mallakar hoto Twitter/@Atiku
Image caption Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar yana cikin wadanda suka halarci taron na PDP

'Yan sabuwar PDP sun yi zargin cewa ba a damawa da su a gwamnatin APC tare da barazanar daukar mataki idan har ba a biya bukatunsu ba.

Sannan a wani bangaren kuma ana tafiya ne da sunan jam'iyya daya amma akwai masu hamayya da juna a APC musamman a jihohi da dama da jam'iyyar ke mulki.

Tasirin kawance a 2015

Wannan abu dai na daya daga cikin manyan al'amuran siyasa da ya faru a Najeriya zuwa yanzu, a yayin da kasar ke shirye-shiryen gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki a watan fabrairun 2019.

Irin wannan al'amari ne ya faru a shekarar 2015 wanda ake ganin shi ne ya janyo shan kayen da jam'iyyar APC ta yi wa tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.

Amma a halin yanzu babu tabbas kan ko wannan gamayyar kawance za ta samu damar cimma manufarta a zabe mai zuwa.

Sai dai masu sharhin siyasa na ganin rigingimun APC da ta ke fama da su na iya yi wa jam'iyyar illa sosai a zaben 2019.