Wa ya fi cin wani tsakanin Faransa da Belgium?

Belgium Hakkin mallakar hoto JEWEL SAMAD
Image caption Masana da dama na ganin Belgium ba ta taba hada kwararrun 'yan wasa kamar wannan karon ba

A ranar Talata ne Faransa za ta fafata da Belgium a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin duniya da ake fafatawa a Rasha.

Duka kasashen biyu, wadanda suka fito daga nahiyar Turai, na kan ganiyarsu a fagen tamola.

Faransa ta fitar da Argentina da kuma Uruguay kafin ta kawo wannan mataki.

Yayinda Belgium, wacce ake ganin ba ta taba hada kwararrun 'yan wasa kamar wannan karon ba, ta fitar da Japan da kuma Brazil a kan hanyarta ta zuwa wannan matakin.

Kasashen biyu sun fafata sau 74 a wasanni daban-daban a tarihi.

Hakkin mallakar hoto JEWEL SAMAD
Image caption Faransa na da kwararrun 'yan wasa wadanda ake ganin suna kan ganiyarsu

Belgium ta fi samun nasara inda ta lashe wasa 30, Faransa ta yi nasara sau 24, sannan suka yi canjaras 19.

Sai dai Faransa ce ta lashe wasa uku na baya-bayan nan da suka yi a manyan kofuna ciki kuwa har da na gasar kofin duniya biyu.

Amma Belgium ba ta yi rashin nasara a wasa uku na sada zumunta na baya-bayna nan da suka yi ba, inda ta samu nasara a wasa daya sannan suka yi canjaras sau biyu.

Nasara ta kusa da ta yi ita ce ta ci 4-3 a watan Junin 2015, inda Marouane Fellaini ya zura kwallo biyu.