'Bullar 'Yan Hakika barazana ce ga tsaro' a Najeriya

President Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Presidency

Ana ci gaba da yada wani bayanin sirri da ke kunshe cikin wata wasika ta kafafafen sadarwa na intanet, a kan bullar wata kungiyar addini mai suna 'Yan Hakika.

Manufar wasikar ita ce ankarar da jami'an tsaro a kan bullar wata kungiyar addini mai suna 'Yan Hakika, wadda ta bulla a jihohin Adamawa da Nasarawa.

Malaman addinin Musulunci na zargin kungiyar tana da'awar cewa yin azumi da sallah ba wajibi ba ne.

Ita wasikar na dauke da tambari sojin Najeriya, amma babu wani bayani da ya fito daga bangaren jami`an tsaro da ya tabbatar da cewa su ne suka fitar da ita.

Duk da haka wasikar na jan hankalin 'yan Najeriya da dama, musamman ma malaman addinin Musulunci, wadanda ke cewa yaduwar wannan akida tana da hadarin gaske.

Tun da farko an yi ikirarin cewa wasikar ta fito ne daga bataliyasar sojin Najeriya ta 192 da ke Gwoza a jihar Borno da ke shiyyar arewa-maso-gabashin kasar .

sojojin na ankarar da sauran jami'an tsaro game da kungiyar da ke karkashin jagorancin wani mai suna Yahaya Ibrahm, wadda wasikar ta ce kungiyar ta fara yada akidarta mai sarkakiya, a jihohin Adamawa da Nasarawa.

A cewar wasikar mai dauke da sa hannun Laftana Janar TG Iortyom, wanda aka ce shi ne mukaddashin kwamandan bataliyar, akidar `yan hakika ta ce yin sallah da azumi ba wajibi ba ne.

Kungiyar ta kuma halatta zina.

Wannan wasika, duk da rundunar sojin Najeriya ba ta tabbatar da cewa daga hannunta ta fito ba, kuma ganin cewa ba ta musanta ba, ta sa wasu 'yan kasar cikin damuwa.

'Kalubalen Tsaron kasa ne'

Sai dai ga malaman addinin musulunci, bullar kungiyar ba ta ba su mamaki ba.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, fitaccen malamin addinin musulunci ne a Kano, wanda ya ce tarihi ne ke maimaita kansa:

"Lalle wannan kungiya, ko addinin Hakika ya bulla a Kano a zamanin marigayi Sarkin Kano Ado Bayero. Sun rika watsa Al Kur'ani a sama, suna cewa babu azumin farilla."

Image caption Wannan na zuwa ne a lokacin da kasar ke cigaba da fafatawa da kungiyar Boko Haram

Sheikh Daurawa ya kara da cewa: A lokacin sarkin ya sa an kama yawancinsu aka daure su a kurkuku."

Ana dai zargin cewa darikar Tijjaniya ce ta haifi `yan hakika. Amma Sheikh Ibrahim Maihula, wakili a hukumar shura ta darikar Tijjaniya ta jihar Kano ya ce hakan ba gaskiya ba ne:

"Wadannan kungiyoyin da suka bulla, ake cewa daga cikin Tijjaniya suka fito - da'awa ce ake yi kawai."

Malaman addainin sun bayyana cewa yaduwar irin wannan akida ta `yan hakika na da hadari a kasa irin Najeriya, idan aka yi la'akari da halin da kasar ta tsinci kanta kamar yadda Sheikh Aminu Daurawa ke cewa.

"Sallolin nan guda biyar an yi ijima'i a kansu, amma wani ya zo ya ce ba dole ba ne a yi su. To kaga wannan yana iya kawo barazanar tsaro a kasa."

Sai dai Sheikh Daurawa ya kara da cewa Najeriya za ta kauce wa irin wannan matsala ta wanzuwar akidun addini barkatai ne, idan ta kafa ma`ikatar da ke kula da harkokin addini.

Labarai masu alaka