An 'kulle' yara kan rashin biyan kudin makaranta a Indiya

Representational image Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani jami'an makarantar ya ce an ajiye yaran ne a wata "cibiyar gudanar da al'amura" amma ba su yi karin bayani ba

'Yan sanda a babban birnin Indiya, Delhi, sun shigar da korafi kan wata makarantar 'yan mata da ta kulle dalibai 16 a ginin da ke can kasan makarantar na tsawon sa'a biyar.

Rahotanni sun ce an kulle yaran ne saboda iyayensu sun gaza biya musu kudin makaranta.

Dukkan daliban da aka kulle din 'yan makarantar renon yara ne (Nursery), wanda suke tsakanin shekaru hudu zuwa shida.

Jami'an makarantar sun ce an ajiye yaran ne a wata "cibiyar gudanar da al'amura" amma ba su yi karin bayani ba.

Iyayen sun ce sun gano an tsare 'ya'yansu ne a lokacin da suke je makarantar don daukarsu amma sai ba su same su a ajujuwansu ba.

Iyayen yaran sun gabatar da korafi ga 'yan sanda, inda suka ce an tsare yaran ne a wani gidan kasa na makarantar daga karfe 7.30 na safe har zuwa 12.30 na rana.

Iyayen sun yi zargin cewa akwai tsananin zafi a wajen da aka tsare yaran, wanda hakan ya sa suka zauna cikin "yunwa da kishi-ruwa".

Wani jami'in 'yan sanda ya shaida wa BBC cewa: "Za mu fidda sunayen mutanen ke da hannu kan abun da aka yi wa yaran bayan mun kammala bincikenmu."

Wasu iyayen sun ce tuni suka biya kudin makarantar. Wani mahaifi ya shaida wa kafar watsa labarai ta intanet NDTV cewa: "Ko bayan da na nuna wa shugaban makarantar shaidar biyan kudin, bai nuna wata nadama ko damuwa ba."

Hukumar kare hakkin yara ta Delhi ta kafa wani kwamiti don gudanar da bincike.

Labarai masu alaka