Hotunan yadda aka ceto yaran da suka makale a kogo
Zakuwar da aka nuna wajen kokarin ceto wata tawagar wasu matasa 'yan kwallon kafa a wani kogo da ya yi ambaliya a Thailand ta ja hankalin duniya.
Mun yi waiwaye kan yadda lamarin ya faru, bayan da aka ceto 'yan samarin na karshe da suka saura da kuma kocin su a ranar Talata.
A ranar Asabar 23 ga watan Yuni ne wasu mambobin wata kungiyar kwallon kafa ta 'Wild Boar' masu shekaru tsakanin 11 zuwa 16 sun shiga Kogon Tham Luang da ke lardin Chiang Rai a kasar Thailand tare da kocinsu bayan da suka kammala atisaye.
Mazauna yankin sun san yadda tsarin kogon mai zurfin kilomita 10 yake, kogo ne mai matsatsi da kuma zurfi sosai.
'Yan wasan sun sha ziyartar kogon a baya, amma a wannan karon ruwan sama mai yawa ya haddasa ambaliya har suka kasa fita.
Bayan da aka ga yaran ba su koma gida ba, sai iyayensu suka kai rahoton batan 'ya 'yan nasu, sai aka fara neman su.
Masu aikin ceto na farko a yankin sun ce sun gano kekunan yaran da takalmansu na kwallo da sauran kaya da ke kusa da kofar kogon.
'Yan jarida da masu aikin sa kai sun taru a bakin kogon duk da ana ruwan sama mai karfi don shawarta yadda za su aiwatar da tsarin ceto yaran.
A ranar Lahadi duk 'yan uwan yaran da sauran mutane sun je bakin kogon suka yi ta addu'o'i.
Bayan da suka shafe kwana uku a kogon, sai masu nutso daga rundunar sojin ruwan Thailand suka je domin taimakawa wajen kokarin bincike.
An samu gano sabbin sawayen hannu da na kafa a cikin kogon, al'amarin ya bai wa mutanen fatan samun yaran da rai.
Jami'an gwamnati sun ziyarci wajen, kuma mataimakin Firai Minista Prawit Wongsuwon ya ce gwamnati ta na sa ran za a samu yaran da rai.
Masu ceto sun yi tunanin bin wasu hanyoyin don shiga ciki- tawagogin sojoji kuma suka ci gaba da neman zabin wasu hanyoyin na fasa dutsen don samun hanya.
A ranar Laraba 27 ga watan Yuni ne wasu kwararrun masu ninakaya daga kasashen duniya daban-daban suka isa Thailand don taimakawa wajen neman yaran.
Iyalan yaran sun ci gaba da yin addu'a a wajen, a yayin da aka ci gaba da damuwa kan abun da ka iya samun yaran. An yi ta daukar hotunan dangin yaran da jami'ai suna suma, da kuma yadda ake ta nuna damuwa kan abun da ka-je-ya-zo na munin yanayi na tsammanin ruwan sama kamar da bakin kwarya.
A hankali dai Thailand ta fara samun sa'ida ganin yadda ake tsaurara bincike, tare da fatan cewa za su tsira. Masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi ta yada sakon girmamawa kan batan yaran inda suke kiransu da "mutanen da muke tsananin son haduwa da su."
An kawo bututan zuke ruwa don rage yawan ruwan da ke cikin kogon, amma ruwan saman da aka ci gaba da yi yana dakatar da kokarin aikin ceton.
Daga baya masu aikin ceto sun yi amanna da fatan cewa tawagar yaran suna cikin aminci a cikin wani surkuku da ke can cikin kogon da ake kira "Patayya beach".
Firai Minista Prayuth Chan-ocha ya ziyarci dangin yaran a wajen kuma ya yi kokarin kwantar musu da hankali tare da ce musu: "Yaran 'yan wasa ne kuma suna da karfin zuciya."
Kafofin watsa labaran duniya duk sun taru a wajen tare da 'yan jaridu duk kuwa da irin tabon da ke wajen, don samun sabbin labarai da dumi-duminsu.
A karshen mako 30 ga watan Yuni an samu ruwan sama ya dan dauke, wanda hakan ya bai wa masu ninkaya damar ci gaba da kutsawa cikin kogon.
An shigar da tulunan shakar iska da wasu kayayyakin bukata a lokacin da masu ceto suka kara samun sararin kutsawa cikin kogon.
A ranar Litinin 2 ga watan Yuli aka samu babban bayani - inda masu ninkiya suka kai wurin da yaran da coachinsu suke cikin halin lafiya, bayan kwana 10 da batan nasu.
A same su a kan wani dutse kusan kilomita hudu daga bakin kogon.
Bidiyon da ke nuna 'yan mazan a cikin koshin lafiya ya fito daga hannun rundunar sojin ruwan Thailand amma jami'ai sun tunasar da cewa karkarin ceto yana ci gaba da bada wahala.
An kai musu abinci da magunguna a yayin da masu aikin ceton ke shawarar yadda za a yi a fitar da su.
An fitar da miliyoyin lita na ruwa daga cikin kogon, amma wani ruwan ya ci gaba da taruwa saboda yanayin damuna da ake ciki, jami'ai sun yi gargadin cewa dole yaran su koti ninkaya kafin a fitar da su - ko su jira tsawon watanni har sai damuna ta janye.
An shiga wani yanayi na damuwa a bakin kogon yayin da daya daga cikin masu ninkaya da ke aikin ceton ya mutu a karshen mako.
An bayyana cewa Saman Gunan mai shekara 38 wanda tsohon sojan ruwa ne da ya zabi yake taimakon sa kai don ceto yara, ya mutu a sanadiyar karewar iska a tukunsa a hanyarsa ta kai musu agaji.
An yi ta bayyana sakonnin yabo da jinjina ga mamacin da kuma nuna damuwa kan yadda ceto yaran zai kasance.
Kwamandan jiragen ruwa na Thailand ya yi gargadin cewa iskar numfashi na kara yin kasa, kamar yadda aka gani a sakonnin da tawagar da kocin suka rubuto.
A lokacin da ake jira ruwan sama ya tsagaita sai jami'ai suka fara tunanin tsara wata mafita da suka yi amannar in an bi za a iya tserar da tawagar.
Da yanayin ya dan fara sauyawa, sai aka yi sa'a aka fara aiwatar da aikin ceton ka-in-da-na'in ranar Lahadi 8 ga watan Yulu
An ga motocin ceto suna barin wurin, abun da ya sa mutane tunanin ko me ya faru da koma yadda ceton ya ke tafiya. Sai daga baya aka bayyana cewa an ceto yara hudu.
Jami'ai sun tabbatar da cewa komai na tafiya lafiya, amma dole ake dakatawa idan dare ya yi domin a cika tulunan iskar sannan masu ceton su huta.
Aikin na da wahala kuma ya hada da tafiya da hawa dutse da kuma ninkiya a gefen igiyoyi da aka riga aka dauwrawa a bango.
A karshen ranar Litinin aka sake fiddoo da wasu yara hudun.
Gwamnatin tana boye bayanai kan yadda aikin ceton ke gudana, ciki har da sunayen wadanda aka ceto.
Ana kai yaran asibiti domin kulawa. An takaita bai wa iyayen yaran damar ziyartarsu a asibiti saboda kare duk wani abu da zai yi barazana ga lafiyarsu.
A ranar Talata aka kara samun cikakken fatan ceto dukkan sauran wadanda suka rage.
Ana ci gaba da aikin ceton a ranar Talata, har sai da aka kammala fiddo da duk yaran 13 da kocinsu.
Mutanen yankin da kuma masu aikin ceto sun yi ta murna, kana daga bisani aka kai yaran da kocinsu asibiti, bayan da suka shafe kwana 17 a cikin kogon da ke karkashin kasa.