Cacar baka ta barke tsakanin Trump da Angela Merkel

Shugabar gwamnati Jamus Angela Merkel na yi wa shugaban Amurka bayani Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Madam Merkel a tsakiya ta jagoranci tattaunawa tare da Shugaba Trump kan kasuwanci a taron G7 da aka yi a makon da ya gabata a Canada

Shugaba Donald Trump na Amurka ya caccaki shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel kan tasirin da Rasha take yi a cikin kasar da kuma kudin da take kashewa tsaro gabanin taron kungiyar tsaro ta Nato da za a yi nan gaba.

Mista Trump ya ce Jamus "na karkashin ikon Rasha" saboda iskar gas da ake shigowa da ita cikin kasar kuma wannan "abu ne mara kyau ga kungiyar Nato".

Madam Merkel ta mayar da martani inda ta jaddada cewa Jamus kasa ce mai cin gashin kai kuma ta kare irin gudumuwar da ta ke bayarwa ga kawancen.

Taron da aka yi a baya wanda ya samu halartar shugabbanin biyu ya bar baya da kura saboda takaddamar da suka rika yi a kan kasuwanci.

Za su sake ganawa a ranar Laraba a birnin Brussels.

Taron na Brussels na zuwa ne kasa da mako guda kafin Shugaba Trump ya gudanar da ganawarsa ta farko da Vladimir Putin a Helsinki, abin da ya sake dawo da fargaba tsakanin kawayen Amurka dangane da kusancin da ke tsakaninsa da shugaban Rasha.

Shugaba Trump ya bai wa wasu mamaki lokacin da ya yi shagube a kan watakila taron Nato ya kasance wani abun wahala fiye da taron da za su yi da Mista Putin a ranar Litinin.

Ya ce kasashen da suke cikin kungiyar da aka kafa a 1949 na amfani da Amurka a matsayin wata dama ta takawa tsohuwar Tarayyar Soviet burki wadda yanzu ta koma Rasha.

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Donald Tusk, ya zarge shi da sukar Turai "kusan a ko wacce rana", inda ya ke wallafa sako a shafinsa na Twitter kamar haka: "Yan uwana Amurkawa, ku gode ma kawayenku, saboda ba ku da abokai masu yawa."

Shin menene Trump ya ce kan Jamus?

Jamus ita ce kasar da ke da karfin tattalin arziki a Turai kuma ta dade tana zargin Amurka da gazawa wajen bayar da gudumuwar a zo agani wajen gudanar da ayyukan NATO, sai dai kalaman Mista Trump ya ta da jijiyoyin wuya.

A taron karin kummalo da aka yi a Brussels tare da shugaban Nato Jens Stoltenberg, shugaban Amurka ya ce: "Jamus na karkashin ikon Rasha saboda suna samun kashi 60 zuwa 70 na makamashinsu daga wurin Rasha, akwai kuma sabon bututun mai, na san za ka ce hakan ya yi dai dai, amma a gan na wannan abu ba alheri bane ga Nato."

Shin menene martanin Angela Merkel ?

"Ina son na ce na san yadda rayuwa ta kasance a lokacin da wani bangare na Jamus yake karkashin ikon Tarayyar Soviet," ta fadawa 'yan jarida.

"Ina matukar farin ciki cewa a yau mun hada kai a matsayin tsintsaya madaurinki daya a matsayin kasa, saboda haka za mu iya tsara manufofinmu tare da yanke shawara. Wannan abu ne mai kyau musaman ga mutanen da ke gabashin Jamus."

Ta kuma kara da cewa Jamus ta tura sojojinta a cikin kawancen tsaro na Nato.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Trump ya tayar da hankalin kasashen Turai gabanin taron da suka yi da Shugaba Putin na Rasha a Helsinki ranar Litinin

Tasirin da watakila Rasha ke yi

Sharhin Jonathan Marcus, wakilin BBC kan tsaro da diplomasiya

Idan za a bayanna Jamus a matsayin "kasar da ke karkashin ikon Rasha" kuma idan za a alakanta lamarin ga abin da Amurka ke kallo a matsayin gibi da ke cikin kasafin tsaro, Shugaba Trump bai dauki batutuwan da Amurka ta dade tana nuna damuwa a kansu da muhimanci ba.

Shugabanin Amurka sun dade suna gargadi kan yadda Turai ta dogara kan Rasha wajen samun makamashi.

Sun kuma shafe shekaru fiye da goma suna fadawa kasashen Turai cewa ya kamata su kara kaso a cikin kudin da aka ware wa tsaro. Sai dai Mista Trump ya yi amfani da kakkausan lafazi kan wadannan batutuwa.

Ko da yake za a iya cewa ya wuce gona da iri kan yadda Jamus ta dogara kan Rasha wajen samun makamashi, saboda akwai shugabannin Turai da dama da sun san irin tasirin da Rasha za ta yi ta haka, yanki ne da manufofin tattalin arziki na gajeren zango da manufofin tsaro na dogon zango suka yi hannun riga da juna.

Shi yasa a lokacin da Amurka ta sanyawa Rasha takunkumi a kan abubuwan da ta ke yi wa Ukraine kuma yankin Crimea ta koma karkashin ikonta, a ciki akwai batun daukar mataki kan duk wani da ya taimakawa Rasha wajen gina sabon bututu zuwa yammaci.

Labarai masu alaka