Ekiti: 'Yan sanda sun sa Ayodele Fayose 'kuka'

Governor Fayose for ground

Asalin hoton, Twitter/@OfficialPDPNig

Bayanan hoto,

Gwamna Ayo Fayose ya zargi 'yan sanda da harba ma sa hayaki mai sa kwalla a ido

Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya yi zargin cewa 'yan sandan jihar na yunkurin halaka shi bayan sun harba hayaki mai sa kwalla a kusa da fadar gwamnati.

Wannan na faruwa ne ana saura kwana uku a gudanar da zaben gwamna a jihar.

Wakilin BBC a sashen Yoruba da ke sa ido a zaben jihar ya ce 'yan sanda da wasu jami'an tsaro sun killace harabar gidan gwamnatin Ekiti, inda suka hana wa magoya bayan gwamnan jihar Fayose shiga.

Gwamna Fayose ya tabbatar da lamarin a shafinsa na Twitter, inda ya wallafa hoton jami'an tsaron tare da cewa 'yan sanda dauke da bindigogi sun toshe hanya domin hana shi gudanar da wani gangamin yakin neman zabe da ya shirya tare da magoya bayan shi.

Sai dai 'yan sanda sun ce babu wani abin da ke faruwa a jihar, "ana nan zaune lafiya," in ji kakain rundunar 'yan sandan jihar.

"Ya kuma ce rundunar 'yan sanda na da alhakin kare lafiya da dukiyar al'umma, shi ne abin da doka ta tanadar mana kuma shi ne abin da muke yi,"

Amma hotunan da suke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna gwamnan a zaune idonsa a rufe kamar ya fita hayyacinsa.

Asalin hoton, @OfficialPDPNig

Bayanan hoto,

Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose

Ya kuma fito a wata kafar talabijin yana kuka, inda ya zargi 'yan sanda cewa sun harba ma shi hayaki mai sa kwalla a idonsa, matakin da ya raunata mutane da dama.

Jam'iyyarsa wato PDP ta wallafa hoton bidiyon da ta dauka a lokacin da gwamnan ke magana a kafar talabijin.

A ranar Asabar ne za a gudanar da zaben gwamna a jihar, zaben da a kullum ke jan hankali a Najeriya musamman tsakanin 'yan takara guda biyu na jam'iyyar PDP mai mulkin jihar da kuma babbar mai adawa ta APC mai mulki a tarayya.

APC da ke mulki a tarayya na kokari ne ta kawar da mulkin PDP a jihar, lamarin da ke iya haifar da rigingimu na siyasa tsakanin bangarorin biyu, kamar yadda ta faru a baya, inda aka kwashe makamai da bindigogi daga hannun magoya bayan 'yan siyasa.

Dubban jami'an tsaro ne aka girke a sassan jihar, kuma rundunar 'yan sandan jihar ta ce ta shiryawa zaben na gwamna da ke tafe a ranar Asabar.