Da gaske ne Donald Trump ya shiga masallacin Harami?

  • Umar Rayyan
  • BBC Hausa, Abuja
Trump

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto,

Saudiyya ce kasar farko da Trump ya kai ziyara tun bayan zamansa shugaban Amurka a shekarar 2017

Wani hoto da ke ikirarin nuna Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya kai ziyara Ka'aba a birnin Makkah na kasar Saudiyya yana ci gaba da daukar hankalin jama'a a kafafen sada zumunta musamman a Najeriya.

Wadansu kafafen sadarwa na intanet ne suka rika yada wannan hoto a kwanakin da suka gabata.

Wasu kafafen sada zumunta da ke kokarin satar bayanai da sunan BBC Hausa ma sun wallafa hoton, abin da ya sa mabiyanmu da dama cikin rudani da kuma tunanin cewa BBC ce ta wallafa labarin.

Bayan wani bincike, BBC ta gano cewa sau daya Shugaba Trump ya taba kai ziyara kasar Saudiyya, wato a watan Mayun shekarar 2017.

Kuma masallacin Harami ba ya daga cikin wuraren da shugaban ya ziyarta a lokacin ziyararsa.

Mene ne asali ko tushen wannan hoton bogen?

BBC ta gano asalin hoton, bayan ta bi sawunsa ta wasu hanyoyi daban-daban.

Wasu ne wadanda da wuya a iya tantance ko su waye suka yanko hoton Trump daga wani hoto, suka jona shi a cikin wannan hoto da ke kasa, wanda asalinsa wani tsohon hoto ne na wadansu manyan 'yan gidan sarautar Saudiyya da malaman kasar suna duba aikin wanke Ka'aba.

Asalin hoton, Al Arabiya

Bayanan hoto,

Wannan ne hoton da aka jirkita don samar da hoton bogen

Kafar yada labarai ta Al Arabiya ce ta wallafa hoton a watan Nuwambar shekarar 2015 - wato kafin ma Shugaba Trump ke nan ya zama shugaban Amurka.

Galibi a kan yi siddabaru da hotuna ne ta amfani da manhajar Photoshop, wanda hakan yake samar da labaran kanzon kurage, musamman a kafofin sada zumunta.

Sai dai wadansu masu mu'amala da kafafen sada zumunta a kasar ba su fahimci hakan ba, saboda sun ta yada hoton bogen Trump da kuma bayyana ra'ayoyinsu game da abin da yake ikirarin nunawa, kamar haka:

Asalin hoton, Facebook

Menene labaran karya?

Sun kunshi bayanai na karya da hotuna da na bidiyo da ake kirkira a yada domin a harzuka mutane.

Ko kuma yada tsoffin hotuna, ko hotunan da ba ma a kasar aka dauka ba.

Irin wadannan labaran karyar da kuma hotunan karyar da ake yadawa, na taimaka wa wajen rura rikici musamman a tsakanin kabilu.

A wasu lokuta rashin samun bayanai daga bangaren gwamnati ko mutanen da abin ya shafa, na haifar da yada jita-jita da kuma zaman dar-dar.

Irin wadannan labaran karya kan haifar da illoli masu yawa, kamar tayar da fitina, da kulla kiyayya tsakanin al'umma da kuma yada bayanan da ba su da tushe.

Binciken da BBC ta yi a kwanakin baya ya gano cewa labaran karya na sahun gaba wurin yada rikicin da ake fama da shi a Najeriya tsakanin makiyaya da manoma.

Hakan ne kuma ya sa ma'aikatar sadarwa ta kasar kaddamar da wani shiri na musamman domin yaki da wannan dabi'a, wacce ke kara samun gindin zama a kasar, musamman a shafukan sada zumunta.

Yadda ake gane labaran karya

Akwai yiwuwar cigaba da samun labaran karya kan wannan rikici, musamman a lokacin da ake tunkarar zaban shugaban kasa a badi.

Kamfanonin sada zumunta kamar Twitter da Facebook sun bayyana shirinsu na yakar sana'ar yada labaran karya a duk fadin duniya, amma ga wasu hanyoyi biyar da za ka iya kawar da yada bayanan da ba su da tushe:

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mutane da dama aka kashe a rikicin manoma da makiyaya wanda aka ce labaran karya na kara zuzutawa

Binciki asalin labarin: Shafukan sada zumunta na karya kan yi kokarin bayyana kansu a matsayin cewa sun fito ne daga manyan kafofin watsa labarai, a don haka ka duba shafi sosai kafin ka watsa bayanan da suka wallafa. Shafukan da aka tabbatar da halaccinsu suna dauke da alamar shudi a Facebook, da Twitter da kuma Instagram.

Duba wasu karin hanyoyin: Duk da cewa wannan wani lokaci ba zai gamsar ba amma yana da kyau a duba abin da wasu kafofin watsa labarai masu inganci ke cewa kan labari domin tabbatar da gaskiyar batu. Tambayi kanka, shin ingantattun kafafan yada labarai na bada rahoton wannan labarin?

Hanyoyin bincika labari: Akwai hanyoyi da dama da za su taimaka maka wurin tabbatar da sahihancin hoto ko bidiyo. Google, da Bing da kuma Tin Eye duk suna duba asalin hoto, wanda kan iya gaya maka inda aka dauki hoto da kuma asalinsa. Tabbatar da bidiyo ya fi wahala amma shafuka kamar InVid na bada damar gano inda aka yi amfani da bidiyon da aka wallafa a Facebook da YouTube a baya.

Duba asalin abin: Idan kana da ainahin hoton ko bidiyo, za ka iya samun bayanai masu muhimmanci game da su, ciki har da wuri da kuma lokacin da aka dauka da kuma na'urar da aka yi amfani da ita. Abin takaicin shi ne da zarar an wallafa hotuna a shafukan sada zumunta to bayanansu na sali sai su bace.

Yi tunani kafin ka wallafa: Dole a yi taka-tsan-tsan saboda ka da a kara jefa mutane cikin rudani. Kafin ka wallafa, ka tambayi kanka ko bayanan da ka ke da su sun inganta kuma ya karfin sahihancinsu ya ke.