An yarda daliba ta sanya hijabi a wurin taron lauyoyi

Amasa Firdaus Hakkin mallakar hoto Bashir Ahmed
Image caption Amasa Firdaus ta ce hakkinta ne sanya hijabi

A karshe dai makarantar koyon aikin lauyoyi ta Najeriya ta amince wa wata daliba ta zama cikakkiyar lauya watanni bayan an hana ta halattar taron saboda ta saka hijabi.

Da farko an shaida wa Amasa Firdaus cewa ba za a barta ta sanya hijabi a kan hular da lauyoyi suke saka wa ba, saboda hakan ya saba wa dokar tufafin makarantar horars da lauyoyin kasar.

Firdaus ta ce hakan ya saba wa 'yan cinta na bil'adama.

Dalibar, wacce ta yi digiri a jami'ar Ilorin ta sanya hular lauyoyin a kan hijabinta a bikin da aka yi ranar Talata domin yaye dalibai 1,550 a Abuja, babban birnin kasar.

Kungiyar Dalibai Musulmii ta Najeriya ta yi marhabin da samun wannan labari, tana mai cewa "makarantar ta nuna dattaku".

Da an hana Firdaus halattar bikin yaye daliban to da "abin ya zama take hakkinta na bil'adama," a cewar kungiyar.

Wani mataimaki ga na musamman ga Shugaba Muhammadu Buhari ya bi sahun wasu 'yan kasar wurin nuna goyon baya da jinjnawa Firdaus:

Labarai masu alaka