Hotunan zanga-zangar da PDP ta yi kan zaben jihar Ekiti

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta kaddamar da zanga-zangar kin jinin abin da ta kira shirin magudin zabe a zaben gwamnan jihar Ekiti da za a yin ranar Asabar.

Image caption 'Yan jama'iyyar adawa ta PDP sun bi manyan titunan birnin tarayyar Najeriya na Abuja don yin zanga-zangar.
Image caption Jam'iyyar PDP din dai ta ce ba ta amince da yadda aka girke dubban 'yan sanda a jihar a Ekiti ba gabannin zaben jihar.
Image caption Masu zanga-zangar sun yi zargin cewa hukumar zabe ta INEC ta dauki ma'aikata masu alaka da dan takarar gwamna a jami'yyar APC domin yin magudi.
Image caption Kazalika masu zanga-zangar sun yi kira ga jami'an tsaron da aka tura jihar ta Ekiti da su kyale mutanen jihar su yi zabensu ba tare da tsangwama ba.

Labarai masu alaka