Buhari ya kaddamar da jirgin kasan birnin Abuja

Jirgin kasan Abuja Hakkin mallakar hoto Presidency

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da tsarin jirgin kasa mai sauki na fasinja da zai dinga zirga-zirga a cikin birnin tarayyar kasar, Abuja.

Shugaban ya kaddamar da jirgin ne a ranar Alhamis, wanda shi ne kashi na farko na wannan aiki.

Hotunan da gwamnatin ta wallafa sun nuna shugaban a babbar tashar jirgin da ke Cibiyar Kasuwanci ta Duniya da ke tsakiyar birnin Abuja.

An shafe shekara 11 ana wannan "gagarumin" aikin tun zamanin mulkin gwamnatocin PDP, amma sai a zamanin Shugaba Buhari aka karasa shi.

A wancan lokacin aikin ya kai kashi 63 cikin 100, inda wannan gwamnatin ta kammala sauran kashi 37 din.

Tsarin jirgin ya kunshi tasoshi 12 a birnin tarayyar.

Hukumomi a Najeriya sun ce jirgin mai tsawon fiye da kilomita 45, shi ne irin sa na farko a yammacin Afirka.

Jirgin kasan zai dinga zirga-zirga ne a cikin birnin tarayyar har zuwa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe.

Sai dai a wata sanarwa da jam'iyyar PDP ta fitar ta ce ita ce ta kirkiro aikin jirgin kasan, "amma ta yi mamakin yadda shugaban ya kaddamar da shi ba tare da yaba mata ba."

Hakkin mallakar hoto Presidency

Labarai masu alaka